For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

NAƊIN MINISTOCI: Tinubu Ya Naɗa Kansa Babban Ministan Mai, Zai Rantsar Da Ministoci Ranar Litinin

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa kansa Babban Ministan Albarkatun Mai na ƙasa yayin da ya naɗa tsohon sanata, Sanata Heineken Lokpobiri a matsayin Ƙaramin Ministan Albarkatun Mai.

Kamar dai yanda ya kasance a shugaban ƙasar da ya yi kafin shi, Muhammadu Buhari, shima Tinubu ya naɗa kansa ministan mai a daidai lokacin da harkar mai a Najeriya ke ci gaba da fuskantar matsaloli.

A jiya Laraba ne dai, Shugaban Ƙasa ya saki sunayen ministoci 46 da muƙamin da ya bai wa kowa, kwanaki tara bayan sanatoci sun kammala tantance su.

Fadar Shugaban Ƙasar ta bayyana cewar, za a rantsar da ministocin ranar Litinin mai zuwa a ɗakin taro na fadar da ke Aso Villa, Abuja.

KARANTA WANNAN: Ƴan Najeriya Na Nadamar Cin Zaɓen Tinubu Da APC, In Ji PDP

A sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey ya saki a jiya Laraba, ya ce, ana buƙatar sabbin ministocin su je wajen karɓar rantsuwar da iya ƴan rakiya bibiyu.

Babban Sakatare na Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya, Lumumba Okugbawa ya ce, babu wata matsala don Shugaban Ƙasa ya zama shine Ministan Albarkatun Man Fetur na ƙasa.

Ya ce, su dai abun da suke buƙata daga gare shi shi ne ya yi ƙoƙari wajen sauƙe nauyin da ya ɗorawa kansa.

Ya ƙara da cewar tun da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya riƙe muƙamin, to shima Tinubu yana da ikon iya yin hakan.

Comments
Loading...