A lokacin da shirye-shiryen shiga babban zaɓen shekarar 2023 ke cigaba da kankama, matashin ɗan siyasa Mustapha Sule Lamido ɗa a wajen tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido ya baiyana aniyarsa ta neman takarar gwamnan jihar a zaɓen shekarar 2023.
Mustapha Sule Lamido ya baiyana aniyar tasa ne a gaban dubunnan magoya baya, a wani taro da aka gabatar a gidansa da ke Babban Birnin Jihar Jigawa, Dutse a jiya Alhamis.
A dogon jawabin da ya gabatar, ya baiyana irin kiraye-kirayen da ya dinga karɓa domin ya fito wannan takara, musamman saboda irin halin ƙuncin da jam’iyyar APC mai mulki ta jefa al’umma a ciki.
Saboda haka ya ce, “Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin Kai. A bisa amana da aka ce a matsayin kira na tafiyarmu gaba daya, ni Mustapha Sule Lamido, na amince zan fito takarar gwamnan Jihar Jigawa.”

Tun a farko, Mustapha ya baiyana cewar jamiyyar APC ta yaudari mutane ne ta hanyar ƙarerayi a lokacin da take neman mulki, inda ya baiyana irin illar da ƙarya ke yi wajen ruguza rayuwar al’umma tare da yin alƙawarin cewa shi ba zai yi ƙarya ba.
Ɗan gidan Sule Lamido mai shekaru 38 a duniya, ya baiyana kasancewarsa matashi a matsayin wata dama ta musamman da matasa zasu samu wajen kawo cigaba a Jigawa, musamman ganin cewa, sune waɗanda suka fi fuskantar matsalolin da ake fuskanta.
Da yake amsa tambayar ƴan jaridu a bayan taron, Mustapha ya nuna cewar fitowarsa ba zata hana sauran ƴan takara fitowa ba, sai dai kuma jam’iyyar PDP za tai amfani da maslaha wajen fito da wanda zai zama gwamnan Jigawa a zaɓen 2023.
A kan batun irin tanadin aiyukan da yaiwa Jihar Jigawa idan ya zama gwamna, Mustapha Sule Lamido ya ce, “eh akwai buri akwai kuma kudiri, amma idan na zama ɗan takarar zan baiyana shi.”
To sai dai kuma a lokacin da yake gabatar da jawabi ga taron al’ummar da suka taru a gidan nasa, ya yi jawabin da yake nuna cewa gwamnatinsa zata shigar da tsarin ilimin tsangaya cikin gwamnati tare da inganta tsarin ilimi a Jigawa.

Mustapha ya kuma kushe tsarin tafiyar da mulki irin na jam’iyyar APC, inda ya ce, “Duk mun san yanda jam’iyyar PDP ta samu Jigawa (a 2007), mun san yanda jam’iyyar PDP ta bar Jigawa (a 2015), kuma mun san yanda APC zata bar Jigawa (a 2023).
“Zai dauke mu tsawon shekaru kafin mu iya dawo da Jihar Jigawa yanda jam’iyyar PDP ta bar ta saboda rashin iya mulki na jam’iyyar APC.”
Mustapha Sule Lamido ya kuma nemi haɗin kan dukkan al’ummar Jihar Jigawa da goyon bayansu wajen samun nasarar kuɓutar da jihar daga mulkin danniya na jam’iyyar APC.