Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce, ya shirya tsaf domin yin yakin neman zabewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da sauran ‘yan takarar jam’iyyar a babban zabe mai zuwa na shekarar 2023.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya Laraba, inda ya ce, Shugaban Kasa ya shirya tsaf domin yakin neman zaben shekarar 2023 da dukkan karfinsa da imaninsa.
Garba Shehun ya kara da cewa, wannan na zuwa ne domin a kawar da shakkun da wasu ke da shi na cewar Shugaban ba ya zuwa guraren yakin neman zaben tun bayan kaddamar da zaben da akai a Jos, Jihar Plateau, inda ya kara da cewa a daidai lokacin da shugaban ke cikin aiyukan jam’iyya, aiyukansa a matsayin Shugaban Kasa suma zasu samu kulawa yanda ya kamata.
Ya kara da bayyana cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana a taron da ya halarta kwanannan a Washington DC cewa, ya shirya tsaf domin yiwa jam’iyyarsa yakin neman zabe domin samun nasararta a babban zaben shekara mai zuwa.
Ya kuma ce, Shugaban Kasar na da karfin guiwar cewa, jam’iyyar APC zata samu nasara cikin adalci a dukkanin zabubbukan masu zuwa.