Daga: DailyTrust
Falmata Abubakar, mahaifiyar marigayi shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ta ce ta yi da na sanin haihuwarsa da tai saboda kasancewar matsala ga al’umma.
Shekau dai ya mutu a watan Mayu na shekarar 2021 bayan ya yi sanadiyyar mummunan yakin da ya jawo mutuwar mutane sama da 100,000 da kuma raba mutane sama da milyan uku da muhallansu da kuma jawo asarar rushe garuruwa, kauyuka, makarantu, asibitoci da sauran kayan rayuwa da akai kiyasin kudin su zai kai sama da Dala Biliyan 9, kamar yanda aka samu a bayanan da suka fito daga jiharsa, kasa da kuma kungiyoyin kasashen waje.
In banda kauyensu, ta’adin da Shekau yai bai ware ‘yan uwansa da ke Borno da Yobe ba, ta’adin ma ya mamaye dukkan al’ummar Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma, Arewa ta Tsakiya da ma sauran sassan Nigeria.
Wannan ne karo na farko da Falmata ta bayyana yanda take daukar danta tun bayan rasuwarsa.
Ta yi magana ne a wata hira ta musamman da Trust TV a kauyenta, Shekau da ke jihar Yobe. Za a saka hirar yau da misalin karfe 7 na dare a kuma maimaita da misalin karfe 10 na dare a Channel 164 Star Times.
An gano cewa, tun lokacin da ya bar kauyensa yana yaro bai kara komawa ba sai wani lokaci da ya je domin ya shigar da al’ummar kauyen cikin Musulunci duk da kasancewarsu wadanda suke yin Musuluncin tun kaka da kakanni.
Kauyen nasau na da tazarar kilomita 50 daga Babban Gida na Karamar Hukumar Tarmuwa a jihar Yobe, haka kuma mafi yawan mutanen kauyen Kanuri ne da Fulani da Mangawa wadanda suka yarda da tsarin zamani suke tura ‘ya’yansu makarantar boko, tsarin da Shekau ke yaka.
“Ban sani ba ko yana da ‘ya’ya,” in ji mahaifiyar Shekau a hirarta da Trust TV.
Falmata ta ce, “kawai haifarsa nai, wannan ce kawai alaka ta da shi. Ko yana raye ko ya mutu, da ma mun raba gari da shi. Ban taba sanin ko yana da ‘ya’ya ba. Ya cusa min matukar bakin ciki. Allah zai sakayya tsakaninmu ranar gobe kiyama.”