For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Naira Ta Ƙara Daraja A Farashin Gwamnati Jiya Litinin

Naira ta samu ƙarin daraja jiya Litinin, inda aka siyar da dala 1 a kan naira 1,339.33 a farashin gwamnati, abun da ya nuna cewar ta samu ƙarin daraja da kaso 9.68 cikin 100 kan yanda darajarta ta kasance a ranar Juma’ar da ta gabata inda aka canjar da dala 1 kan naira 1,482.81.

Bayanan da FMDQ wadda ke kulawa da hada-hadar canjin kuɗaɗe a Najeriya ya nuna cewar, cinikin canjin kuɗaɗen da aka yi a jiya Litinin ya yiwo ƙasa zuwa dala miliyan 180.80 daga dala mililyan 556.25 da aka samu a ranar Juma’ar da ta gabata, abun da ke nuni da raguwar kaso 67.50 cikin 100.

A jiya Litinin ɗin farashin naira na gwamnatin kan dalar mafi tsada shine naira 1,501 kan dala 1 yayin da mafi araha ya kasance naira 1,310 kan dala 1.

A kasuwar bayan fage kuma, a jiya Litinin ɗin an canja dala 1 ne kan naira 1,520, abun da ke nuna faɗuwar darajar naira da kaso 1.32 cikin 100 kan naira 1,500 da aka canjarta a ranar Juma’ar da gabata.

Comments
Loading...