Daga: Lukman Dahiru
Marigayi Sir Abubakar Tabawa Balewa Firaminista na farko kuma na karshe, a ranar 1 ga watan Octoba 1960 ya bayyana cewa “al’umar Najeriya sunyi naam da nasarorin da kasar ta samu na yawan jamaa da fadin kasa, tare da bada tabbacin bata da wani gilli ko manufa ga wata kasa ko yanki kasancewar takasa mai cikekken ‘yanci’.
A irin wannan rana dole ne a dinga tinawa da mutanen da sukayi gwagwarmaya domin tabbatuwa kasar dake Kudu da Sahara.
Mutane irin su Sir Abubakar Tabawa Balewa, Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, Murtala Muhammad, Malam Aminu Kano da Yakubu Gawon da sauransu, na daga cikin wadanda suka taka rawar gani wajen tabbatuwar Najeriya a matsayin kasa guda.
Ya zuwa yanzu najeriya tana da yawan al’umma sama da miliyan 200, kabilu da addinai daban-daban.
Matsalar tsaro na daya daga cikin abubuwan da suka yiwa kasar katutu musamman a yankunan Arewa da sauran sassa, matsalar koma bayan tattalin arziki, da cin hanci da rashawa.
Sai dai masana alamuran yau da kullum irin su Farfesa Kamilu Sani Fagge na ganin anci gaba sai dai matsaloli nan da can da baza a rasa ba; “har muka kai ga yakin basasa watanni 30, amma har yanzu muna zaune a matsayin kasa daya duk da irin banbance-banbancen da muke dasu na siyasa, addini da kabilu”.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jawabin da ya gabatar a ranar 1 ga watan Oktoba 2021 ya hori yan kasa da dunkulewa waje daya a matsayin al’umma daya.
Amma masu fafutukar tabbatar da adalci da mulki na gari sunyi amanna da cewa matsalar Najeriya bai wuce rashin shugabanci na gari ba, irin su Marigayi Dan Masanin Kano Dr Yusuf Maitama Sule tsohon Ministan Manfetur na Najeriya a jamhuriya ta farko, da Sir Abubakar Tafawa Balewa Firaminista na farko.
“A dukanin irin wannan yanayi zakaji ana ambaton sunayen wadanda suka bautawa kasa ba don abauta musu ba, suka gama mulki batare da sata ba gudun talauci, basu azurta kansu da yayansu da dukiyar kasa ba, basu mai da matasa ‘yan jagaliya ba, basu kwashi dukiyar kasa da sunan albashi ba, basu bata wasu ba dan su samu mulki, basa rayuwar karya da arzikin kasa,” in ji Danmasanin Kanon.
Tambaya; shin yan kasa da shugabanni me suke yi wa kasar?
Ya batun kishin kasa a zukatan mu?
Shin muna yi? Zamu yi? Ko munyi?
Masu iya magana sunce ‘da zanyi, da inayi duk nayi tafi su’.
Lukman Dahiru
Ya Rubuto Daga KUST, Wudil