Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce burin Najeriya na kasancewa hadaddiya ba mai girgizuwa ba ne.
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya ce duk da kalubalen da ake fuskanta, Najeriya za ta ci gaba da kasancewa a dunkule.
Ya bayyana hakan ne yayin bude taron nuna hotuna domin shirin murnar zagayowar ranar samun ‘yancin Najeriya mai taken “Shekaru 60 na Hadin Kan Mu, ” a ranar Litinin.
A cewar Ministan: “An shirya baje kolin hotunan a tsari don nuna hadin kan wannan babbar kasa a cikin shekaru 60 da suka gabata, duk da bambancin al’adu, dabi’u, ayyuka, harsuna da kuma kalubaloli.
“Kamar sauran kasashe na duniya, abu ne da ba za a iya mantawa da shi ba cewa, Najeriya a cikin shekaru, ta shiga cikin lokutan kalubale, amma bai kamata mu rasa fata na kasancewa daya daga cikin abubuwan da ba za a iya raba su ba”.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jagororin ‘yan aware, Nnamdi Kanu da Sunday Igboho ke ta tayar da kayar baya.
Yayin da jami’an tsaron Najeriya suka kama Kanu, shi kuma Igboho na kulle a Jamhuriyar Benin.
A halin da ake ciki, Lai Muhammed ya ce Ma’aikatarsa na amfani da damar da bikin ranar samun ‘yancin kan ta bayar don shirya baje kolin hotunan.
Ya ce baje kolin an yi shi ne don fadakarwa da ilmantar da matasan Najeriya kan tarihin kasar, abubuwan gado na musamman, da sirrin da ke tattare da hadin kan kasar a fannoni daban -daban.