Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya ce, Najeriya na bukatar mutanen kirki su zama ‘yan tawaye domin su ciyar da ita gaba.
Obasanjo ya ce, mutanen da suke gudanar da rayuwa cikin gaskiya da amana ya kamata su zama ‘yan tawaye, inda ya kara da cewa, rikon amana da gaskiya suna sanya mutum ya zama mai fadawa shugabanni gaskiya ba tare da tsoron kowa ba.
Tsohon Shugaban ya yi wannan magana ne jiya a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun a taron kaddamar da littafin tarihin Babanla Adinni na kasar Egba, Cif Tayo Sowunmi a matsayin wani bangare na bikin murnar cikarsa shekaru 80 a duniya.
Littafin tarihin da akaiwa suna da “Footprints Of A Rebel,” Hafsat Abiola, ‘yar marigayi dan siyasa MKO Abiola kuma wadda ta kirkiri gidauniyar “Kudirat Initiative for Democracy” ce ta duba littafin.
Obasanjo ya baiyana cewa, samun mutane masu gaskiya matsayin ‘yan tawaye, wata gagarumar gudummawa ce ga ciyar da kasa gaba.
Ya kuma yabi tsohon mai shekaru 80 a duniya saboda rayuwar gaskiya da ya gudanar wadda ta zama abar koyi ga ‘yan yanzu.
“Duba da sunan littafin, Na tambayi kai na, me yasa wani zai kira kansa da dan tawaye? Amma hakan yana da kyau.
“Amma kuma gaskiyar magana ita ce, idan kana son ka yi rayuwa ta gaskiya da amana, akwai bukatar ka zama dan tawaye. Akwai lokutan da za a bukaci ka yi wani abu, amma za ka ce a’a wannan bai dace ba. Kuma idan ka ce haka, ka zama dan tawaye. Za ma ka iya zama mai bakin jini.
“Babu wata kasa da za mu kira tamu in banda Najeriya. Kasarmu Najeriya tana bukatar karin ‘yan tawaye. Wadanda za su kalli al’amura kai tsaye su ce ‘wannan bai dace da Najeriya ba’, in ji Obasanjo.
(THE NATION)