Kungiyar Magoya Bayan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, yayin da take murnar cikar Najeriya shekaru 61 da samun ‘yancin kai, ta bayyana cewa kasar na ci gaba da komawa baya a karkashin mulkin Shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren Yada Labarai na kungiyar, Dr El Mo Victor, kungiyar ta ce wannan gwamnatin ta sarayar da murnar bikin samun ‘yancin kai.
Sanarwar ta ce, “Ta yaya za mu yi murnar samun ‘yancin kai a yau yayin da Najeriyar a shekara 61 ta kasance cibiyar talauci ta duniya tare da shigar da yanayin rayuwar ‘yan kasarmu cikin matsananciyar kunya?
“Ta yaya za mu yi murna alhali sama da kashi 55.7% na‘ yan Najeriya ba su da aikin yi ko suna aikin da bai biyan bukatunsu, kuma da kyar suke iya ciyar da iyalansu da biyan kudin makarantar ’ya’yansu?
“Ta yaya za mu yi murna, yayin da mafarkin matasan Najeriya ke rugujewa tare da yin watsi da hakikanin damarsu a wannan gwamnatin da ta gaza ta APC karkashin jagorancin Muhammadu Buhari?”
Victor, yayin da yake fitar da wasu kididdiga, ya yi ikirarin cewa kusan yara miliyan 13 a Najeriya ba sa zuwa makaranta.
Ya yi tambayar cewa, “Ta yaya za mu yi bikin, yayin da sama da yara miliyan 13 na Najeriya ba sa zuwa makaranta, mafi yawa a Kudu da Sahara kuma sama da yawan mutanen kasashe kamar Laberiya, Namibia, Botswana, da Gabon?
“Ta yaya za mu yi biki yayin da tattalin arziki ya lalace tare da canjin Naira a Dala ya kai $ 1/N587, hauhawar farashin kayayyaki a kasuwa ya hau sama da kaso 300 zuwa 800% fiye da yadda talaka zai iya jurewa? A shekaru 61, an saka Najeriya a cikin manyan kasashe shida da suka fi talauci a duniya da ke fama da matsanancin bashi.
“Ta yaya za mu yi bikin farin ciki yayin da yanayin tsaro a Najeriya a shekara ta 61 ke cikin mummunan yanayi, kuma a duniya, Najeriya ta haura Afghanistan da Iraki cikin jerin kasashe masu ta’addanci? Daga shekarar 2015 zuwa yau, sama da mutane 100,000 da ba su ji ba, ba su gani ba ‘yan ta’adda, da masu garkuwa da mutane suka kashe. Gwamnati ba ta iya komai kuma ta kasa aiwatar da ainihin aikinta na kare jama’a.”
Kungiyar Magoya Bayan Atikun ta yi amfani da wannan dama don karfafawa matasa gwiwar shiga siyasa domin ‘yantar da al’umma.
“Ta yaya za mu yi biki yayin da tushenmu yai rauni? Maimakon samun hadin kai, Najeriya a shekara ta 61 tana da rarrabuwar kawuna da rarrabuwa ta hanyar kabilanci da addini?
“Kasar tana bukatar iskar shaka, kuma dole ne matasa su tashi don ‘yantar da al’umma daga wannan gwamnatin da APC ke jagoranta, sannan kuma a 2023 a kawo mai gina kasa kuma jagora wanda ya fahimci tattalin arziki kuma zai iya amfani da damar da matasa ke da ita a Najeriya don gina kasa mai wadata ga dukkan mu.”