Daga: BBC Hausa
Majalisar Zartarwa ta gwamnatin tarayyar Najeriya ta ware naira tiriliyan 348.7 a matsayin kuɗin da za a kashe a Shirin Cigaban Ƙasa (Naitional Development Plan).
Ministar Kuɗi da Kasafi Zainab Ahmed ce ta bayyana haka jim kaɗan bayan kammala zaman da majalisar ta yi ranar Laraba, wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.
Zainab ta ce shirin na shekara biyar zai maye gurbin Economic Recovery and Growth Plan (ERGP) wanda zai ƙare a Disamban 2021.
An tsara shirin zuwa aji shida da suka haɗa da haɓaka tattalin arziki da cigaba, da ayyukan raya ƙasa, da shugabancin al’umma, da taimaka wa rayuwa, da ciyar da al’umma da yankuna gaba.
A cewarta, gwamnatin tarayya za ta faɗaɗa karɓar haraji sannan ta ƙarfafa ɓangaren ‘yan kasuwa ta hanyar sama musu damarmaki da zummar samun kuɗin gudanar da shirin.
Shirin ya yi hasashen za a samu haɓakar ma’aunin tattalin arzikin Najeriya da kashi 5 cikin 100, inda hukumomin gwamnati za su samar da biliyan 49.7 yayin da ɓangaren ‘yan kasuwa zai samar da tiriliyan 298.3.
Kazalika, daga cikin shirin za a tsago kasafin kuɗin ƙasa.