For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Najeriya Ta Ayyana Talata A Matsayin Ranar Hutun Maulidi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata 19 ga watan October, 2021 a matsayin ranar hutu domin bikin mauludi na bana.

Wannan ya zo ne domin taya murnar zagayowar ranar haihuwar Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammadu SallalLahu Alaihi wa Sallam.

Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayyar Najeriyar ta cikin wata sanarwa da babban sakatare a maaikatarsa, Shuaibu Belgore, ya fitar.

Aregbesola, ya taya al’ummar Musulmin Najeriya na cikin gida da wadanda ke kasashen waje murnar samun damar ganin ranar mauludin ta bana.

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su koyi da halayyar son juna da juriya wadanda duk halaye ne na Manzon Allah, Annabi Muhammadu SallalLahu Alaihi wa Sallam, wanda hakan kuma shine zai tabbatar da zaman lafiya da samuwar tsaron kasa.

Ministan ya hori ‘yan Najeriy, musamman Musulmi da su kaucewa halayyar tayar da hankali, rashin bin doka da ma duk sauran munanan halaye.

Comments
Loading...