Babban Bankin Najeriya (CBN) a ranar Alhamis, ya ba da sanarwar dakatar da shirin kaddamar da tsarin kudi na intanet wanda aka fi sani da eNaira, don ba da damar aiwatar da wasu muhimman ayyuka na tunawa da ranar cika shekaru 61 da samun ‘yancin kan.
Da yake magana da manema labarai a Abuja, kakakin babban bankin na CBN, Mista Osita Nwanisobi, ya bayyana cewa CBN ya dauki matakin jinkirta kaddamarwar ne, wanda da farko an shirya ta zo daidai da ranar samun ‘yancin kai, bisa fatan kara samun hadin kan Najeriya a matsayin kasa daya.
Yayin da yake tabbatar da cewa babu wani abin tashin damuwa game da dakatarwar, ya ce CBN da sauran abokan hulda suna aiki dare da rana don tabbatar da tsari mai kyau wanda zai kasance cikin fa’idar abokan ciniki gaba daya, musamman ga wadanda ke yankunan karkara da kuma mutanen da ba su da banki.
Da yake haskaka fa’idojin eNaira, Nwanisobi ya ce ‘yan Najeriya za su iya aiwatar da canjin-sa-kai zuwa walat ɗin eNaira na wani tare da biyan kaya da ayyuka ga ‘yan kasuwa. Ya kara da cewa eNaira zai kuma taimaka wajen rage amfani da tsabar kudi da tabbatar da kwanciyar hankali ga tattalin arzikin Najeriya.
Dangane da shirye -shiryen bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade don kaddamar da eNaira, ya ce eNaira tsari ne daki-daki, yana mai bayanin cewa ba duk masu amfani da banki bane ake sa ran za su fara ma’amala daga ranar farko da aka kaddamar.
Nwanisobi ya kuma yi bayanin cewa CBN na sane da damuwar da aka bayyana game da eNaira, kasancewa irinsa na farko a duniya. A cewarsa, bankin ya sanya tsari mai kyau don magance duk wata matsala da ka iya tasowa daga aiwatar da eNaira.