For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Najeriya Ta Nada Kwamitin Magance Rikicinta Da ASUU Wanda Zai Gabatar Da Rahoto Cikin Wata 3

Gwamnatin Tarayya ta samar da kwamiti mai mutum 7 wanda zai kara duba yarjejeniyar Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU da Gwamnatin Tarayya ta shekarar 2009.

Kungiyar ASUU dai ta shiga yajin aikin gargadi na wata 1 tun ranar 14 ga watan Fabrairun da ya gabata, saboda dambarwar gazawar gwamnati na cika alkawuran da ta yiwa kungiyar.

Da yake kaddamar da kwamitin jiya a Abuja, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya bukaci ‘yan kwamitin da su sake dubawa tare da  yin abun da zai yiwu game da yarjejeniyar ASUU da Gwamnatin Tarayya ta shekarar 2009.

Kwamitin dai yana da Pro-Chancellor na Alex Ekwueme Federal University, Ndufu-Alike, Farfesa Nimi Briggs a matsayin shugaba.

Sauran manbobin kwamitin sun hada da Pro-Chancellor na Federal University, Wukari, Lawrence Ngbale a matsayin wakilin Arewa maso Gabas; Pro-Chancellor na Federal University, Birnin Kebbi, Farfesa Funmi Togunu-Bickersteth a matsayin wakilin Kudu maso Yamma; da Pro-Chancellor, na Federal University, Lokoja, Sanata, Chris Adighije a matsayin wakilin Kudu maso Gabas.

Sauran sune Pro-Chancellor na Federal University of Technology, Minna, Farfesa Olu Obafemi a matsayin wakilin Arewa ta Tsakiya; Pro-Chancellor na Kano State University of Science and Technology, Farfesa Zubairu Iliyasu; da kuma Pro-Chancellor na Niger Delta University, Wilberforce Island, Matthew Seiyefa daga yankin Kudu maso Kudu.

Minista Adamu ya tunawa ‘yan kwamitin cewa sake duba yarjejeniyar ASUU da Gwamnatin Tarayya ta 2009 an fara ta tun a ranar Litinin 13 ga watan Fabarairu na shekarar 2017.

“To amma saboda wadansu abubuwa da ba a zata ba, da suka hada da annobar korona, aikin ya samu tsaiko ya kawo har yanzu. Babbar bukatar duk wani mai ruwa da tsaki a harkar ilimi da dukkan kasa gaba daya shine a gaggauta kammala sake duba wannan yarjejeniya cikin kankanin lokaci.

“Saboda haka, ina kira ga wannan kwamiti da ya kara azama wajen kammala aikin da aka ba shi tare da fito da tabbatattun matsaya kuma mai yiwuwa wadanda za su magance matsaloli su kuma yi tasiri wajen cigaban kasa”.

Ministan ya kuma ce, kwamitin zai hada guiwa tare da tuntubar masu ruwa da tsaki da suka da ce domin fitar da matsayar karshe ta Gwamnatin Tarayya kan yarjejeniyar ASUU da Gwamnatin Tarayya ta shekarar 2009.

Ya kara da cewa, kwamitin zai kuma tantance tare da baiyana sauran abubuwa da za su temaka wajen bunkasa tsarin jami’o’i domin yin gogaiya da sauran na duniya, rahoton da za a gabatar cikin watanni uku masu zuwa daga ranar da aka ƙaddamar da kwamiti.

Minista Adamu ya kuma ce, “Tabbas nadinku ku yiwa Gwamnatin Tarayya aiki a wannan mataki yana da alaka da gagarumar gudummawar da kuke bayarwa wajen cigaban jami’o’i. Saboda haka, bana tantamar cewa za ku yi wannan aikin cikin kwarewa da kuma gaggawa yanda ake bukata.”

Comments
Loading...