Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Najeriya, TCN, ya baiyana cewa, samar da wutar lantarki a kasar ya fado kasa wanwar saboda matsaloli a tashoshin samar da wutar guda 14.
Kamfanin ya nuna cewa, samar da wutar a watanni biyu da suka gabata ya nuna cewa tashoshin gas guda 14 ko dai ba sa aiki gaba daya ko kuma aikin nasu bai taka kara ya karya ba.
Mai magana da yawun TCN, Ndidi Mba ya ce, wannan matsala ta ta’azzara matsalar karancin wutar lantarkin da ake rarrabawa ‘yan kasa a kowacce rana.
Wannan na faruwa ne a lokacin da kaiwa ‘yan kasa karin kudin wutar lantarkin da aka yi karkashin tsarin Service Based Tariff, SBT.
An kirkiro tsarin SBT ne da nufin cewa wutar lantarkin zata karu, amma maimakon hakan lamarin samuwar wutar ya kara tabarbarewa.
‘Yan Najeriya da dama na fama da duhu yayin da suke cigaba da korafin biyan ninkin kudin wutar da suke biya watanni biyu ba.
Lissafi dai ya nuna cewa, ana cajar ‘yan Najeriya naira biliyan 720 duk shekara na kudin wutar lantarki, abinda ya nuna cewa, cikin shekaru 8 da suka gabata ‘yan Najeriya sun biya naira tiriliyan 5.7 a matsayin kudin wutar lantarki.
A yanzu dai wutar Najeriya ta ragu matuka inda Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ke raba wutar mai karfin megawatts 1,145 a yanzu sabanin megawatts 4,000 da ake da karfin iya rarrabawa.