Daga: Kabiru Zubairu
Majalissar Zartarwa ta Najeriya Federal Executive Council (FEC), ta amince da bayar da kwanaki 14 ga mazajen da matansu suka haihu domin samun damar kulawa da jariran da suka haifa ko suka karba domin riko.
Wannan hutun na maza ne kawai wadanda ke aiki a ma’aikatun gwamnatin tarayyar Najeriya.
Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan ce ta bayyana hakan, a jawabin da ta gabatar ga manema labarai jim kadan bayan kammala zaman Majalissar Zartarwar Kasar na Larabar nan wanda Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya jagoranta.
Dr Yemi-Esan, wadda ke tare da Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu na Kasar, Alhaji Lai Mohammed, ta bayyana cewa an amince da bayar da hutun ne ga mazan da matansu suka haifa musu jarirai.
Ta ce wannan karramawar tana da amfani domin a temaki wadanda aka haifar ko wadanda aka karba domin riko tare da samar musu shakuwa da mahaifinsu a farkon lokaci.