For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Najeriya Za Ta Gabza Da Afrika Ta Tsakiya

Daga: Muhammad Yobe

A Alhamis din nan ne da misalin ƙarfe 5 na yamma qungiyyar ƙwallon ƙafa ta Nigeria Super Eagles zata fafaata a cigaba da wasannin samun gurbin na buga gasar cin kofin duniya na 2022 da za’ayi a qasar Qatar.

Amma a wannan karon qasar zata buga wasannin na ta 2 ne babu wasu manyan ƴan wasa irin su, Wilfred Ndidi, Alex Iwobi, Ebuchi, Zaidu Sunusi, Samuel Chukueze saboda fama da rauni.

Karawar ita ce ta uku a cikin rukunin da Super Eagles za ta yi wasa biyu a jere gida da waje da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, inda za su kara ranar 7 ga watan Oktoba a Teslim Balogun a Legas, sannan su buga wasa na hudu cikin rukuni a Doula ranar Lahadi 10 ga watan Oktoba.

Kawo yanzu Super Eagles tana da maki shida a wasa biyun da ta yi nasara a kan Liberiya da kuma Cape Verde a farkon watan nan.

Ita dai Jamhuriyar Afirka ta tsakiya na buga wasanninta a Kamaru a matsayin gida.

Ga jerin ƴan wasan da Nijeriya za tayi amfani da su:

Masu tsaron raga: Francis Uzoho (AC Omonia, Cyprus); Daniel Akpeyi (Kaizer Chiefs, South Africa); Maduka Okoye (Sparta Rotterdam, The Netherlands)

Masu tsaron baya: Chidozie Awaziem (Alanyaspor FC, Turkey); Kenneth Omeruo (CD Leganes, Spain); Leon Balogun (Glasgow Rangers, Scotland); William Ekong (Watford FC, England); Olaoluwa Aina (Torino FC, Italy); Jamilu Collins (SC Padeborn 07, Germany); Abdullahi Shehu (AC Omonia, Cyprus); Calvin Ughelumba (Glasgow Rangers, Scotland); Kevin Akpoguma (TSG Hoffenheim, Germany)

Masu buga tsakiya: Frank Onyeka (Brentford FC, England); Joseph Ayodele-Aribo (Galsgow Rangers, Scotland); Innocent Bonke (Malmo FF, Sweden); Alex Iwobi (Everton FC, England); Kelechi Iheanacho (Leicester City, England)

Masu cin qwallo: Ahmed Musa (Fatih Karagumruk, Turkey); Samuel Kalu (FC Bordeaux, France); Victor Osimhen (Napoli FC, Italy); Moses Simon (FC Nantes, France); Paul Onuachu (KRC Genk, Belgium); Chidera Ejuke (CSKA Moscow, Russia).

Comments
Loading...