For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Najeriya Za Ta Kara Daukar ‘Yan NPOWER 490,000

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jawabinsa na samun ‘yancin kai a ranar Juma’a ya ce, ana ci gaba da gudanar da shirye-shiryen zabo wasu mutane 490,000 da za su ci gajiyar shirin NPOWER.

A cewarsa: “Idan aka yi la’akari da kyakkyawan tasirin da shirye-shiryen mu na Zuba Jari kan Jama’a ya yi, kwanan nan na amince da a kara masu cin gajiyar shirin N-Power daga 500,000 zuwa 1,000,000.

“Daga cikin wadannan, 510,000 suna cikin shirin, yayin da ake shirya tsarin zaba cikin fitattun wasu masu cin gajiyar su 490,000.

Comments
Loading...