Gwamnatin Tarayya a ranar Laraba ta nuna alamun cewa za ta kashe tiriliyan N6.258 a cikin kasafin kudin shekarar 2022 wanda za ta ciyo bashi.
Ministar Kudi, Kasafin da Tsare-Tsare ta Kasa, Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana hakan ga manema labarai na fadar gwamnati bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) na mako, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Fadar Shugaban Kasa, Abuja.
Ministar, wanda ke tare da Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami, da Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Muhammed, sun kuma bayyana cewa FEC ta amince da kudirin kasafin 2022, wanda yawansa ya kai N16.39 tiriliyan.
A cewar Zainab, abubuwan da ake son cimmawa a gwamnati ba za su samu cimmuwa ba ba tare da an ciyo bashi ba.
Ta kuma ce duk da cewa ana nuna damuwa kan yawan bashin da gwamnatin ke karba, amma ta kawar da fargabar cewa lamarin na iya yin kamari, tare da bayyana cewa har yanzu basussukan na Najeriya suna cikin iyakokin da suka kamata.
“Idan muka dogara kawai da kudaden shiga da muke samu, duk da cewa kudaden shigar mu sun karu, kudaden gudanar da ayyukan gwamnati, gami da albashi da sauran abubuwa ba za su yiwu ba.”
“Don haka, muna buƙatar bashi don samun damar yin waɗannan ayyukan da za su tabbatar da cewa mun samu haɓaka.