Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da bayar da tallafi ga daliban da ke karatun digiri a fannin ilimi (education) da kuma masu karatun NCE.
Gwamnatin ta sanar cewa, za ta bayar da Naira 150,000 ga dalibai masu karatun digiri a fannin ilimi duk shekara, yayin da za a bayar da Naira 100,000 ga masu karatun NCE su ma duk shekara.
Minsitan Ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya sanhar da haka a jawabinsa da ya gabatar a Abuja kan Ranar Malamai ta Duniya ta shekarar 2021.
Ministan ya ce an dawo da tsarin ne bayan sakamakon Kwamitin Gudanarwa na Kasa da gwamnati ta kafa bayan maganar Shugaban Kasa ta kudirin sake fasalin harkar ilimi da koyarwa a kasar a jawabinsa na Ranar Malamai ta Duniya ta shekarar 2020.
Ya ce ma’aikatarsa za ta hada kai da ma’aikatun ilimi na gwamnatocin jihohi 36 da kuma Abuja domin ganin an tabbatar da shirin.
Za a gano kwasakwasan da ake bukata ga kowacce jiha, sannan “wadanda za su mori tsarin dole su kasance a makarantun gwamnati kadai tare da kuma sanya hanun kan yarjajjeniyar yiwa gwamnati aiki na shekaru 5 bayan kamala karatunsu.”
“Za a samu kudaden gudanar da shirin daga UBEC, TETFund sannan kuma Hukumar Bayar da Tallafin Karatu ta Kasa za ta kula da shirin.”
Minista Adamu Adamu ya ce ma’aikatarsa za ta hada kai da hukumomi da kungiyoyi irinsu NTI, TRCN, CPN, NUC, NCCE, UBEC, PTDF, TETFund da kuma kungiyoyi masu zaman kansu domin shiryawa da kuma bayar da horo kan koyarwa da kuma fasahar zamani ga malamai da kuma ma’aikata a makarantu.
Ya bayyana cewa, “Hukumomin UBEC, TETFund and PTDF za su temaka wajen samar da kudaden gabatar da horon duk shekara.”
“Gwamnati za ta hada kai wasu hukumomi na musamman kamar bankin Federal Mortgage Bank na Nigeria, tsarin bayar da bashi na Federal Government Staff Housing Loans Board, FGSLB, tsarin samar da walwala na FME Staff Welfare, da kuma kungiyar NUT domin samar da gidaje masu sauki ga malaman makaranta.”