Wani Baturen Netherlands wanda ya debe shekaru 55 a Najeriya, Cif Joop Berkhout a jiya Alhamis, ya yi Allah-wa-dai da harin jirgin ƙasan da ƴan bindiga suka kai ranar Litinin din da ta gabata a Kaduna.
Baturen ɗan shekara 92, wanda ya baiyana Najeriya a matsayin gida a wajensa ya ce, yanayin da Najeriya ta tsinci kanta a ciki a lokacin yakin basasa ya fi dadi sama da abin da ƴan Najeriyar ke ji a yanzu.
Bature Berkhout wanda ya cika shekara 92 a jiya Alhamis, ya baiyana hakan ne a tattaunawarsa da DAILY TRUST a matsayin wani ɓangare na murnar karin shekarunsa da aka yi a Ibadan babban birnin Jihar Oyo.
Ya ce, gagarumar matsalar da ke addabar ci gaban buge-bugen takardu a Najeriya ita ce shigowa da kayan aikin buga takardun da ake yi.
Jaridar DAILY TRUST ta rawaito cewa, a matsayinsa na Babban Darakta na farko a kamfanin buga litattafai na Evans Brothers, a shekarar 1967, kafin daga bisani ya kirkiri Spectrum Books Ltd., a shekarar 1978, Baturen wanda aka haifa a Amsterdam ya samawa kansa daukaka da girmamawa a tsakanin mawallafa da kuma malamai a Najeriya.
Ya baiyana cewa abin da kawai ƴan Najeriya ba sa shigowa da shi wajen haɗa littattafai shine basira, abin da a fadarsa ya ta’azzara tsadar littattafan a ƙasar.
Baturen wanda ya baiyana ƴan Najeriya a matsayin masu tsananin kaifin basira da kuma karamci, ya bayar da shawarar cewa mutane suna haifar waɗanda zasu iya ɗaukar ɗawainiyarsu.
Berkhout wanda aka baiwa sarautar gargajiya ta Okun Borede na Ile-Ife saboda gudunmawar da yake baiwa sashin ilimi na Najeriya ya ce, lokacin da yai ritaya daga aiki a Spectrum Books a shekarar 2008, yana ɗan shekara 78, ya gaza dena cigaba da aikin buga litattafai saboda kaunarsa da harkar.
Ya ce, “Najeriya ta canja kuma ba canji mai kyau ba. Abin da ya faru a ƴan kwanakin nan a Najeriya abin Allah-wa-dai ne. Babu wani waje a duniya da mutane ke kaiwa filin jirgin sama hari. Babu wani waje a duniya da mutane ke kaiwa jirgin ƙasa hari. Yanzu haka hatsari ne ka ce zaka je Kaduna. An rufe filin jirgi na Kaduna saboda matsalar tsaro.
“Haka ma jirgin ƙasa ya tsaya daga Kaduna zuwa Abuja. Ko a lokacin yaƙin basasa (yaƙin Biafara) yanayin ya fi na yanzu da muke ciki daɗi. A lokacin yaƙin basasa, mutane na iya tafiya ko ina a Najeriya. Zan iya barin Ibadan da misalin ƙarfe 6 na yamma na je ko’ina ta kan titi. A wannan lokacin ina tafiya dare da rana.
“Matsalar Najeriya talauci ne da kuma yawan jama’a. Ya kamata mu ilimantar da mutanenmu da su dena haifar yaran da ba zasu iya lura da su ba. Waɗansu zasu ce maka ai yara baiwa ce daga Allah amma ba hakan ba ne. Mutanenmu ya kamata suna la’akari da yawan ƴaƴan da suke son haifa tun kafin su yi aure. Idan ka yi loma da abin da ya fi karfin bakinka zaka samar da talauci.”
(DAILY TRUST)