For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Nan Da 2026, Biyan Bashin Najeriya Zai Iya Laƙume Kuɗaɗen Shigar Ƙasar Gaba Ɗaya Idan Ba A Yi Hattara Ba – IMF

Asusun Bayar da Lamuni na Ƙasa da Ƙasa, IMF ya yi gargaɗin cewa, biyan bashin da Najeriya ke yi, zai iya laƙume kuɗaɗen shigar 100 bisa 100 nan da shekarar 2026 idan har gwamnati ta gaza ɗaukar matakan da suka kamata na haɓɓaka samun kuɗaɗen shiga.

Wakilin IMF a Najeriya, Ari Aisen ne ya baiyana hakan jiya a Abuja, lokacin da yake da rahoton tattalin arzikin kasashen Afirka na Kudu da Hadar Sahara.

Ya ce, bisa la’akari da sakamakon ƙaramin gwajin kudaden da aka mu’amala da su a shekara da akai, biyan kuɗin ruwan bashin da aka ciyo zai iya laƙume kafatanin kuɗaɗen da ƙasar ke samu cikin shekaru huɗu masu zuwa.

An gano cewar, a farkon wannan shekarar, Gwamnatin Tarayya ta kashe naira tiriliyan 4.2 domin biyan bashi tsakanin watan Janairu zuwa watan Nuwamba na shekarar 2021, wanda ke wakiltar kaso 76.2% na naira tiriliyan 5.51 da ƙasar ta samu a lokacin.

Gwamnatin Tarayyar kuma ta shirya kashe naira tiriliyan 3.61 wajen biyan bashin Najeriya a kasafin kuɗin shekarar da muke ciki, abin da ya kai kaso 34% na kuɗaɗen da ake sa ran Gwamnatin Tarayya zata samu a shekarar.

Yawan bashin da ake bin Najeriya, wanda yawansa ya kai naira tiriliyan 39.56 a watan Disamba na shekarar 2021, zai iya kai wa naira tiriliyan 45.95 duba da shirye-shiryen Ofishin Kula da Bashi na ƙasar na ciyo ƙarin bashin naira tiriliyan 6.39 domin cike giɓin da za a samu a kasafin kuɗi na shekarar 2022.

Da yake magana a Abujan, Aisen ya baiyana damuwarsa kan cewa, ƙasashen Afrika da dama, ciki har da Najeriya, na fuskantar barazanar faɗawa cikin rikicin biyan bashi, har sai in an ɗau matakan ƙara hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.

A kan Najeriya, Aisen ya ce, wannan yanayi ya samo asali ne daga ƙarancin samun kuɗaɗen shiga na ƙasar, saboda haka, akwai buƙatar samar da ƙarin kuɗaɗen shiga domin a samu ci gaban tattalin arziki.

Ya ƙara da cewa, wannan muhimmin abu ne ga Najeriya.

Ya kuma yi ƙorafin cewa, duk da kasancewar ƙasar mai fitar da mai, amma Najeriya ta kasa ɗaukar matakan morar hauhawar farashin man fetur da ke faruwa a duniya saboda tallafin da take sanyawa a ɓangaren.

Aisen ya ce, kuɗaɗen biyan tallafin mai na Najeriya, zasu iya kai wa naira tiriliyan 6 zuwa ƙarshen shekarar nan da muke ciki da dai irin kuɗaɗen da ake warewa na rabin tiriliyan a duk wata domin tallafi kaɗai.

Haka kuma, ya baiyana yardarsa cewa, Matatar Ɗangote zata rage shigowa da mai Najeriya, idan har an kammalata, kuma hakan zai rage yawan adadin kuɗaɗen da ake kashewa a tallafin.

Ya ƙara da cewa, ƙamarin hauhawar farashi da babban zaɓen shekarar 2023 zasu ƙara zama barazana ga tattalin arzikin Najeriya.

Aisen ya kuma ce, “Matsalar tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa, musamman ƴanbindiga da garkuwa da mutane da kuma zaɓe mai ƙaratowa a shekarar 2023 zasu shafi ƙoƙarin tattalin arzikin ƙasar.

A jawabinsa, Darakta Janar na Ofishin Kula da Basussuka na Ƙasa, Ben Akabueze, ya nuna rashin yarda da lissafin Aisen na alaƙar da ke tsakanin samun kuɗaɗen shiga da kuma biyan bashi, inda kuma ya yarda da cewa, Najeriya na kashe kuɗaɗe da yawa wajen biyan bashin.

Comments
Loading...