Mai neman takarar Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, a jiya Litinin ya baiyana a gaban kwamitin tantance ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, domin ya kare muradinsa na tsayawa takara domin ya gaji Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a 2023.
Tantancewar na gudana ne karkashin kwamitin da tsohon Gwamnan Jihar Edo kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, John Oyegun ke jagoranta a Hotel din Transcorp Hilton a Abuja.
Wasu daga cikin tambayoyin da akai wa jagoran APC, Tinubu, sun shafi batun tasowarsa, neman iliminsa da kuma kwarewar da ya samu, kamar dai yanda Daraktan Yada Labarai da Sadarwa na Yakin Neman Zaben Tinubu, Bayo Onanuga ya fada.
“Cikin karfin guiwa ya fadawa masu tantancewar cancantarsa ta yi wa APC takarar shugaban kasa,” Onanuga ya fada. “Ya bayar da misali da irin nasarar da ya samu lokacin da yana Gwamnan Legas, inda samun kudaden shiga ya tashi daga Naira Miliyan 600 duk wata zuwa Naira Biliyan 51 a yanzu haka.”
Na kusa da Tinubun ya ce, dan takarar shugaban kasar ya kuma nuna yanda zai samar da wadatacciyar wutar lantarki a Najeriya.