For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Nau’in Omicron Na Iya Canza Yanayin Yaki Da Cutar Korona – Ghebreyesus

Babban daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana cewa, wasu daga cikin siffifon nau’in Omicron, ciki har da yaduwarsa a duniya, da kuma yadda yake yawan sauyawa, sun nuna cewa, nau’in zai iya yin babban tasiri kan yanayin cutar ta Korona.

Tedros ya bayyana haka ne jiya Laraba, yayin wani taron manema labarai, inda ya yi gargadin cewa, nau’in na Omicron zai iya kara yaduwa fiye da ragowar nau’in cutar ta Korona, ganin yadda ya zuwa yanzu ya yadu zuwa kasashe 57.

A cewar babbar masaniyar kimiya a hukumar WHO Soumya Swaminathan, har yanzu lokaci bai yi ba, da za a ce nau’in na Omicron zai iya rage tasirin rigakafin cutar.

Daga: CRI Hausa

Comments
Loading...