Hukumar Kula da Kafafen Yada Labarai ta Kasa, NBC ta hukunta gidan talabijin na Arise TV da tarar naira miliyan 2 saboda yada labaran kanzon kurege da suka shafi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Alla Progressives Congress (APC), Bola Tinubu.
A wata wasika mai dauke da kwanan wata 13 ga Nuwamba, wadda Babban Daraktan NBC, Balarabe Ilelah ya sanya wa hannu, ya ce kafar talabijin din ta sabawa ka’idojin yada labarai.
Gidan talabijin na Arise TV, a baya dai ya bayar da hakuri bisa yada labaran karya wanda ya ce, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC na bincikar Tinubu kan zargin safarar miyagun kwayoyi.
“Hukumar Kula da Kafafen Yada Labarai ta Kasa ta sanya hukuncin tarar naira 2,000,000.00 a kan Arise TV, a matsayin hukunci kan karya dokar yada labarai ta Najeriya,” in ji wasikar ta NBC.
“A ranar Asabar 12 ga watan Nuwamba, 2022, hukumar ta duba anfani da takardar yada labarai wadda Festus Okoye, Esq, Kwamishinan Kasa kuma Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa da Arise TV ta yi.
“Wannan takardar yada labarai ta yi zargin cewa, INEC na bincikar al’amarin da ya shafi kwace kudin da kotun Amurka ta yi daga wajen dan takarar shugaban kasa na APC domin yanke hukunci. Takardar an yi mata tambari da ‘labaran karya’ amma kafar (Arise TV) ta samar da wata takardar wadda ke musa wannan maganar.
“Za a iya tuna cewa, a tsakanin 19 da 26 ga watan Satumba, 2022, NBC ta zagaya kasar nan domin wayar da kan kafafen yada labarai da kuma tunasar da su tanade-tanaden dokokin yada labarai na Najeriya da kuma Dokar Zabe a lokacin da muke tunkarar babban zaben 2023. Hukumar kuma ta kalubalanci masu yada labarai da ta sake tantance gaskiyar labarai, musamman ma wadanda suke fitowa daga kafafen sadarwa, abun da aka tabbatar a Sashi na 5.6.5 na Dokokin Yada Labarai na Najeriya.
“Haka kuma, mun jawo hankali kan Sashi na 5.0.1 na Dokokin Yada Labarai na Najeriya wanda ya ce, ‘Dole a tabbatar labarai na gaskiya ne kuma na daidai kan abu ko lamarin da ya faru . . . Labarai na bukatar kwarewa daga bangaren masu yada shi wajen biyayya ga ka’idojin aikinsu. Wadannan sun hada da tabbatar da gaskiya, daidai, adalci, rashin son kai . . .’
“Haka kuma, Sashi na 5.1.3 na dokar ya ce, ‘AN HARAMTA LABARAN KARYA’ ‘Labarai shine mafi karfi a duk abubuwan yadawa, saboda haka, aikin mai tantance labarai wani gagarumin aiki ne. Dole ne a tantance duk wani labarai.”
Hukumar ta kuma gargadi duk masu yada labarai da su yi biyayya ga tanade-tanaden Dokokin Yada Labarai na Najeriya.