For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

NCC Ta Jaddada Ranar Karshe Ta Hada SIM Da NIN

Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC ta ce nan ba da jimawa ba wadanda ba su shaidar zama dan kasa ta NIN za su rasa damar samun abubuwa da dama a Najeriya ciki har da Lasisin Tuki da kuma Fasfo.

Haka kuma hukumar ta jaddada ranar 31 ga watan Oktoba a matsayin ranar karshe ta hada lambobin layikan waya da lambar NIN.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa mai taken ‘Hada NIN da SIM: NCC Na Wayar da Kan Masu Amfani da Hanyoyin Sadarwa a Ranar 31 ga Watan Oktoba’ wanda Daraktan Hulda da Jama’a na NCC, Dr. Ikechukwu Adinde ya sanya wa hannu, ranar Laraba.

Sanarwar ta kara da cewa, “NCC ta tunatar da kuma bukatar masu amfani da hanyoyin sadarwa da su hada NIN din su da SIM din su kafin karewar wa’adin 31 ga Oktoba, 2021 da Gwamnatin Tarayya ta sanya.”

Sanarwar ta kara da cewa, “Da yake magana yayin shirin kai tsaye, Daraktan Hulda da Jama’a na NCC, Dakta Ikechukwu Adinde, ya shawarci ‘yan Najeriya da su yi amfani da tsawaita aikin hade NIN da SIM zuwa 31 ga Oktoba, 2021, don yin rajista tare da hukumar NIMC domin samun NIN da kuma hada su da SIM din su.”

Adinde ya ce, “Ba da dadewa ba, mutanen da ba su da NIN za su rasa damammaki masu mahimmanci wadanda ke taka muhimmiyar rawa a rayuwarsu gami da samun lasisin tuki, fasfo.”

Shima da yake magana cikin shirin, Daraktan NCC na Ofishin Kasuwanci, Efosa Idehen, ya ce, “Za a iya amfani da layikan SIM din da ba a hada da NIN ba wajen aikata laifukan da ba za a iya gano su ba.”

Comments
Loading...