For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

NDLEA Ta Gargadi Masu Keke NAPEP Akan Safarar Kwayoyi Da Masu Fataucin Mutane

Shugaban NDLEA, Brig.-Gen. Buba Marwa, a ranar Asabar a Abuja ya gargadi masu tuka babur, wanda aka fi sani da Keke NAPEP ko Adaidaita Sahu kan daukar masu safarar miyagun kwayoyi.

Marwa ya ce za su yi asarar jarinsu idan aka kamasu suna amfani da baburansu wajen safarar masu fataucin muggan kwayoyi ko abubuwan haram a kowane yanki na kasar.

Shugaban na NDLEA ya yi gargadin ne lokacin da babban birnin tarayya FCT da shuwagabannin jihohi 36 na Tricycle Owners Association of Nigeria (TOAN) suka kai masa ziyarar girmamawa.

A cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da bayar da wayar da kan jama’a na NDLEA, Mista Femi Babafemi ya fitar, shugaban ya jaddada bukatar kungiyar ta tabbatar da cewa ba a yi amfani da baburan wajen safarar miyagun kwayoyi ba.

A cewar Marwa, “ku da miliyoyin membobinku kun saka miliyoyin kudi don yin wannan sana’a.

“Amma bari in yi kira da gargadin cewa da yawa daga cikin membobinku na iya rasa jarin su idan an kama su da amfani da baburansu da temakawa masu laifi, ta hanyar amfani da su wajen safarar miyagun kwayoyi da masu safarar miyagun kwayoyin.

“Don Allah ku roki mambobinku wadanda ke yin hakan da su daina saboda hukumar NDLEA za ta riske su kuma za su zargi kansu ne kawai,” in ji Marwa.

Shugaban na NDLEA ya bayyana shirye -shiryen Hukumar na yin hadin gwiwa da kungiyar don ilmantar da membobinta da fasinjojinsu kan illolin muggan kwayoyi da kuma ilimin sanin hanyoyin tona asiri.

Tun da farko, kungiyar wacce ta samu wakilcin shuwagabannin shiyyoyinta bakwai sun bukaci hadin gwiwa da NDLEA a yaki da shan miyagun kwayoyi da fataucin muggan kwayoyi.

A nasa jawabin, jagoran tawagar, Kwamared Aliyu Shuaibu, ya yi godiya ga Marwa bisa yadda ya saurari ‘yan kungiyar duk da yawan ayyukan da yake da su.

Shuaibu ya lura cewa kimanin ‘yan Najeriya miliyan 40 ne ke cin gajiyar kai tsaye ko ta wani fannin daga harkar baburan.

Ya ce ban da neman hadin gwiwa da NDLEA kan yaki da miyagun kwayoyi, kungiyar ta kuma yabawa Marwa.

Shuaibu ya yabawa Marwa kan kokarinsa na kawo sana’ar baburan Keke NAPEP Najeriya lokacin yana gwamnan Legas.

“Irin da ka shuka a jihar Legas shekaru da suka gabata shine abinda ke raya miliyoyin ‘yan Najeriya har zuwa yau, a matsayin kasuwanci da hanyar sufuri.

“Mun zo nan ne don mu gode maka saboda wannan babban hangen nesa; muna kuma nan don tallafawa aikinku na yanzu na yaƙi da haramtattun kwayoyi da fataucin mutane.

“Kuma a lokaci guda don nada ka a matsayin Babban Uba na TOAN.

Shuaibu ya ce, “Wannan ya samo asali ne daga irin gudummuwar da kake bayarwa wajen gina kasa, musamman ga harkar baburan Keke NAPEP, wanda a yau shine tushen rayuwar miliyoyin ‘yan Najeriya kuma mafi arahar hanyoyin sufuri ga talakawa,” in ji Shuaibu.

(NAN)

Comments
Loading...