For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyi Na Kimanin Naira Biliyan 2 A Lagos Daga India

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA sun kama codeine mai nauyin kilogram 40,250 wanda kudinsa ya haura naira biliyan 2, an shigo da shi a kontenoni guda biyu manya daga kasar India.

Wannan kame ya zo bayan ‘yan kwanaki da aka yi wani makamancinsa wanda aka kama ruwan codeine mai nauyin kilogram 14,080 da kuma maganin tari mai nauyin kilogram 4,352.43 wanda aka boye codeine din a ciki a wata babbar kontena shi ma daga kasar India a ranar 2 ga watan Fabrairu, 2022 a Lagos.

Mai magana da yawun Hukumar NDLEA, Femi Babafemi ne ya tabbatar da cigaban a jiya Alhamis ga manema labarai.

Ya ce, dukkanin kamen ya samo asali ne daga rahoton sirri da hukumar ta samu daga abokan huldarta na kasashen waje da kuma hadin guiwar da ma’aikatan gabar teku suke bayarwa, wadanda suka hada da jami’an Hukumar Hana Fasa Kwauri, jami’an Hukumar Leken Asiri, Sojojin Ruwa na Najeriya da sauran su.

Babafemi ya yi bayanin cewa, an kama kayan kusa-kusan nan ne a ranar 8 ga Fabarairu wadanda aka kawo a kontena mai lamba: HLBU 2239792, dauke da katan 1,125 na codeine, da kuma kontena mai lamba HLBU 1067338, dauke da katan 1,751 na codeine, wadanda akai kiyasin kudinsu a naira biliyan 2 da miliyan 12 da naira dubu 500.

Ya kuma baiyana kayayyakin a matsayin wadanda suka sabawa doka.
(PUNCH)

Comments
Loading...