Shugaban Hukumar Hana Sha da Fatucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, Buba Marwa, ya amince da kara wa’adin sati guda kafin a rufe shafin daukar sabbin ma’aikata na hukumar.
Buba Marwa ya bayyana hakan ne a sanarwar da Daraktan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na hukumar, Femi Babafemi ya fitar a jiya Alhamis a Abuja.
Sanarwar ta bayyana cewa, an yi karin ne domin bayar da dama ga masu neman aikin wadanda suka sami tasgaro a kokarinsu na cike neman aikin.
An dai bude shafin daukar sabbin ma’aikatan ne a ranar Lahadi, 12 ga watan Maris, inda aka tsara rufe shi a gobe Asabar, 8 ga watan Afirilu, 2023.
To amma yanzu da karin sati gudan da NDLEA ta yi, za a rufe shafin daukar ma’aikatan ne da misalin karfe 11:59 na daren ranar 17 ga watan Afirilu, 2023.
NAN