Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO) a yau Alhamis ta saki sakamakon jarabawar kammala sikandire (SSCE) ga wadanda ba ‘yan makaranta ba (external students) wadda aka rubuta a watan Nuwamba da Disamba na shekarar 2021.
Haka kuma NECO ta kori wasu masu kula da yanda ake gudanar da jarabawar guda hudu saboda mummunan aikin kula da jarabawa.
Rijistaran NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi wanda ya saki sakamakon ya ce, masu duba jarabawar da akaiwa hukuncin, daya ya fito daga jihar Niger daya daga Borno yayinda sauran biyun suka fito daga jihar Delta, inda ya kara da cewa an yi hukuncin ne domin magance matsalar magudin jarabawa.
Wushishi ya baiyana cewa, cikin mutane 47,916 da sukai rijistar zana jarabawar, mutane 45,821 suka rubuta jarabawar English inda mutane 36,116 cikinsu suka sami credit zuwa sama a darasin.
Rijistaran ya kuma baiyana cewa, mutane 29,342 cikin wadanda suka rubuta jarabawar sun sami credits 5 zuwa sama a English da Mathematics da sauran darussa, yayinda mutane 37,991 suka sami credits 5 zuwa sama amma babu English da Mathematics.
Wushishi ya ce, an sami raguwar mutanen da aka zarga da magudi a jarabawar, inda aka sami korafi 4,454 a shekarar sabanin korafi 6,465 a shekarar 2020.
Ya kuma baiyana cewa, ana kokari wajen ganin an bunkasa harkar jarabawar domin samun karin inganci ta kowanne bangare.
(ThisDay)