A cigaba da bayar da damar neman aikin a Hukumar Hana Fasakwauri ta Kasa, Customs, ta bude damar neman aikin a yau Laraba 15-12-2021 ga masu shaidar karatun Diploma da NCE domin neman matsayin Inspector Cadre AIC, (CONSOL 06).
A wannan bangare hukumar ta bayar da damar nema ga masu shaidar kammala karatun na Diploma ko NCE a kowanne fanni.
Hukumar ta fara da bayar da damar ne ga masu karatun digiri na farko ko babbar diploma da su nemi aikin a matsayin Superintendent Cadre ASC II (CONSOL 08) tun a ranar Litinin 13-12-2021.
Hukumar ta sanya ka’idojin cike neman aikin kamar haka:
Dole ne mai neman ya kasance dan Najeriya
Kar tsayin me neman ya gaza mita 1.7 ga maza, da kuma mita 1.6 ga mata.
Mai neman ya kasance yana da fadin kirjin da bai kasa da mita 0.89 ba.
Ya kasance yana da shedar kasancewa lafiyayye a jiki da kwakwalwa daga likitan gwamnati.
Kar ya zama yana fama da jinya a jikinsa ko a kwakwalwarsa.
Ya kasance wanda ba ya cikin rikicin kudi da zai zubar masa da mutunci.
Ya zama mai kyakkyawan hali kuma wanda ba a kama da aikata laifi ba a kotu.
Ya kuma kasance wanda ya iya amfani da na’ura mai kwakwalwa.
Ya kasance yana da shedar kasancewa dan karamar hukumarsu wadda shugaban karamar hukumar ya sanyawa hannu.
Mai neman kuma kar ya haura shekaru 30 a duniya.
Hukumar ta kuma yi gargadi na musamman ga masu amfani da takardun bogi, kan cewa ba za ta lamunci hakan ba.
Za a bayar da damar ga masu shaidar karatun sikandire domin neman matsayin Assistant Cadre CA, II, III (CONSOL 03, 04) ranar Jumu’a 17 ga watan da muke ciki.
Jaridar Jakadiya Press za ta kawo muku ka’idojin da za a sakawa masu shaidar NCE, Diploma da kuma sikandire da zarar an saka su.