For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Nigeria Na Bukatar ‘Yansandan Jihohi Domin Magance Matsalar Tsaro – Obasanjo

Daga: PUNCH

Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, akwai bukatar kirkirar ‘yansandan jihohi domin magance matsalar tsaron da ke addabar kasar nan.

Obasanjo ya bayyana cewa, za a iya gina kasa ne kawai idan gwamnati ta sami damar bayar ingantaccen yanayi ga ‘yankasa.

Tsohon shugaban ya yi wannan maganar ne a ranar Juma’ar nan a Lagos a wajen wani taron gabatar da lakcoci da ya gabatar da lakca mai taken ‘Gudunmawar Al’umma Wajen Ciyar da Kasa Gaba’ a taron bikin zagayowar Island Club na 78.

Ya bayyana cewa, “Na taba fada a baya kuma zan kara fada. Ya kamata Nigeria ta samu ‘yansandan jihohi saboda su magance matsalar tsaro. Tabbatarwa da ‘yankasa lafiyayyen yanayin wajen zama da ingantaccen tsaro wani abu ne da ya zama wajibi a kan gwamnati.

“Babu wata kasa da za ta ginu a inda tsaro da kwanciyar hankali ba su samu ba ko ba su tabbata ba haka kuma hasashen shugaban kasa da na makomar kasa ba su tabbata ba.”

Obasanjo ya kuma ce, gwamnatin da ta kasa sauraron ‘ya’yanta to ta dau hanyar rugujewa.

Ya kara da cewa, “Duk gwamnatin da ta kurumce, bebance ta kuma makance to gwamnati ce da ba za ta dade ba. A matsayi na gwamnati, ya kamata ta saurari jama’a. Idan ka kasa sauraron jama’a, to ranar da-na-sani za ta zo ma kuma da wurwuri. Za mu iya ganinta, har ma ta zo.

“Ya kamata ka san cewa akwai abubuwan damuwa a cikin rayuwa. Me zai hana ka yin magana? Jin tsoro? Akwai karin maganar Yarabawa da yake cewa ‘Kai magana ka mutu, ka ki magana ma ka mutu’ saboda haka mutuwa dole ce. Kamar yanda kuka ganni a nan, ni ba na tsoron mutuwa.

“Abin takaici ne abubuwan da muke gani. Yanzu haka akwai yaran da ba sa makaranta sama miliyan hudu a Nigeria. Wannan gaskiya ce, ba za su iya boye ta ba. Babu dan Nigeriar da zai kare kuskurensu saboda tsoron mutuwa. A fadi gaskiya; idan za su ki to su ki karba.”

Ya yi kira ga ‘Yannigeria da su rungumi banbance-banbancensu su yi aiki a matsayin ‘yankasa daya domin ciyar da dunkulalliyar Nigeria gaba.

Ya ce, “Banbance-banbance daga Allah yake; haka kuma daga Shedan. Mu a matsayinmu na ‘Yannigeria, ya kamata mu koyi yanda za mu magance matsalar banbance-banbacen mu, ta haka ne za mu samu manufa daya a matsayin makomar Nigeria. Kasa ba ta ginuwa har sai da sadaukarwa da fahimatar juna da kuma bayar da gudunmawa da samarwa komai manufa mai kyau.”

Comments
Loading...