For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Nigeria Na Kokarin Magance Gibi Tsakanin Farashin Dala Na Gwamnatin Da Na ‘Yan Kasuwa

Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Kasa, Zainab Shamsuna Ahmad, ta bayyana cewa ma’aikatarta na hada guiwa da Babban Bankin Najeriya domin rage gibin da ke tsakanin farashin Dala na gwamnati da farashin Dala na ‘yan kasuwa ta hanyar habbaka yalwar samuwar kudaden waje.

Wannan ya fito ne a wata hira da Ministar tai da BLOOMBERG, inda ta ce Gwamnatin Tarayya na nufin bunkasa hanyoyin samun kudaden shiga ta amfani da sananniyar hanyar nan ta mai da iskar gas.

Minista Zainab, ta yi cikakken bayan ikan bashin da yake kan Najeriya da kuma yanayin kashe kudade a kasar.

A cewarta, ma’aikatar kudi na hada kai da Babban Bankin Najeriya domin cike gibin da ke tsakanin farashin dala na gwamnati da kuma na ‘yan kasuwa.

“Fatanmu ne mu samu damar rage gibin da ke tsakanin farashin da ba na gwamnati da kuma farashin gwamnati. Haka kuma, abin da za mu yi shine mu bunkasa hanyoyin samun kudaden waje, Yanzu haka sananniyar hanyar da ake yin hakan ita ta amfani da mai da kuma iskar gas,” in ji Zainab.

Ministar ta bayyana cewa, kudaden shiga suna karuwa sai dai kuma kashe kudaden na karuwa sama da karuwar kudaden.

“Muna da matsalar samun kudade, kuma muna aiki domin magance matsalolin kashe kudaden ta hanyar takaita kashe kudaden a ma’aikatu da kashi 50% na kudaden da suke samu,” in ji ta.

Ta kara da cewa, idan Matatar Mai ta Dangote ta fara aiki a shekarar 2022, Najeriya za ta samu damar alkinta kaso 30% na abin da take kashewa yanzu a kan mai, sannan kuma za ta samu Karin shigowar kudaden waje ta hanyar siyar da albarkatun mai ga kasashe makwabta.

Ministar ta ce “idan aka kwatanta bashinmu da kudaden shigarmu za mu ce ya yi yawa. Akwai kudade da yawa daga kasafin kudinmu da suke tafiya wajen biyan albashi, kuma Shugaban Kasa ya yanke shawara tun a farkon lokacin mulkinsa cewa ba za mu kori ma’aikata ba. Saboda haka dole a biya albashi, dole a biya fansho. Haka kuma dole a baiwa sauran turakan gwamnati kudade, wadanda sune bangaren shari’a da kuma majalissa.”

Comments
Loading...