Makarantar Nigerian Air Force school of Medical Sciences and Aviation Medicine sun fidda sanarwa sayar da form.
wannan makaranta tana cikin Jihar Kaduna kuma an kirkirota a shekarar 2019.
Ga dukkan masu son shiga wannan makaranta a bangaren Diploma ko National Diploma, ND ko Higher National Diploma, HND a wannan shekarar karatu da muke ciki, wannan makaranta zata bawa jami’an soja wanda suke bukatar karin karatu da wanda ba soja ba da Kuma wanda suke bukatar zama sojoji.
Abubuwan da ake buƙatar mai neman wannan makaranta ya tanada sun hada da:-
- Credits biyar 5 a WAEC, NECI ko NAPTEB, sannan 5 din su zamana a English, Mathematics, Physics, Chemistry da Biology, kuma dole ya zama wannan credits an same sune a cikin zaman jarabawar da bai wuce biyu ba.
- Ana buqatar masu sha’awar shigar da kar su gaza shekara 16 sannan kar su haura 28 kafin watan Oktobar shekarar nan.
- Dole ne masu neman shigar su zama yan kasar Nigeria ta haihuwa.
- Masu neman shigar su kasance sun rubuta jarabawar JAMB ta shekarar 2021 ko ta shekarar 2022 sannna ya kasance sun samu maki a kalla 120.
A Ina Za A Samu Application Form?
Application form za a same shi ne a ofishin Rijistrar na makarantar sannan a kwai biyan kudi naira dubu goma sha biyar (15,000).
Bayan cikewa za a mayar da application zuwa ofishin Sakatariyar rijistrar hadi da photocopies na takardu, a kalla sati daya kafin aje wajen jarabawar shiga.
Ranar ranar jarabawar shigar zata kasance 5 zuwa 8 ga watan Satumba na wannan shekarar ta 2022.
Domin tuntubar wannan makaranta sai a kira wadannan lambobi da ke kasa.
09019116990
08144482671
09011050632
