Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPC, ya kara tabbatar da cewa, ya rarraba wadataccen man fetur wanda zai magance matsalar karancinsa da kuma tsadarsa a kasar.
NNPC ya baiyana hakan ne a jiya Juma’a da daddare.
NNPC ya kara da cewa, ya hada kai da duk masu ruwa da tsaki da kuma jami’an tsaro domin ganin cewa an magance matsalolin da ke jawo tsaiko wajen isar man sassa daban-daban na Najeriya.
Tun da farko dai NNPC ya baiyana cewa ya tanadi man fetur kimanin lita miliyan 387.5 domin magance karancin man da kuma dawo da farashinsa kan na ka’ida.