Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya amince da cewa yana da ɗinbin bashi a kansa na masu kawo man fetur, wanda ya kai dala biliyan 6, wanda ya ce shi ne babban dalilin da ya haifar da karancin fetur a sassan ƙasar nan.
Kamfanin ya taba alaƙanta matsalar da batutuwan dabarbaru da bala’o’in yanayi kamar ambaliyar ruwa a baya, amma yanzu ya bayyana cewa matsin bashin na barazana gacigaba da rarraba man fetur a faɗin kasa.
Duk da wannan ƙalubale, NNPCL yana nan kan matsayinsa na samar da man fetur shi kaɗai ga Najeriya, bisa dokar Masana’antar Mai don tabbatar da tsaron makamashi na kasa.
Dogaron Najeriya kan shigo da albarkatun mai da aka tace daga waje, tare da rashin aiki na matatun mai na gwamnati, ya ƙara tsananta matsalolin man, inda layukan shan man fetur suka zama ruwan dare.
Bayan cire tallafin fetur a watan Mayu 2023, farashin fetur ya ninka sau uku, wanda ya kara wahala ga ‘yan Najeriya da ke dogara da fetur a motocinsu da janareto, musamman duba da rashin tabbas na wutar lantarki a ƙasa.
NNPCL ya ce, yana aiki tare da hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki domin dawo da wadatar man fetur da kuma magance matsalar da ake fuskanta.