For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Noman Citta Zai Bunkasa Arzikin Matasan Jigawa – Ado Maje

Shugaban Kungiyar Manoma Citta ta Kasa reshen jihar Jigawa, Comrade Ado Maje Saleh (Retd), ya bayyana cewa, noman citta zai zama sanadiyyar arzutar matasa kusan dubu daya a jihar Jigawa a shekarar nan.

Ado Majeh ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Taskar Yanci, inda ya ce matashi yana bukatar kudi naira 800,000 ne wajen noma kadada daya, yayinda bayan ya cire cittar zai samu ribar kusan miliyan 3 a noma daya.

Gonar Citta

Ado Maje ya kara da cewar kungiyarsu ta manoma citta a Jigawa ta kammala duk shirye-shirye wajen wucewa matasa 250 gaba daga kowacce karamar hukuma cikin kananan hukumomi 27 da ke jihar.

Kungiyar za ta wuce musu gaba wajen samun bashin kudin jarin noman, inda ya tabbatar da cewa, tattaunawa ta yi nisa tsakanin kungiyar da Babban Bankin Najeriya, CBN da kuma gwamnatin jihar Jigawa kan lamarin.

A saboda haka ne ma, Ado Maje ya ce, kungiyar za ta fara yiwa masu sha’awar shiga shirin noman cittar rijista a Jigawa a kwanan nan.

A karshe ya mika godiya ta musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar bisa amsa kiran kungiyar da kuma alkawarin wucewa matasan gaba domin a cimma nasara.

Ado Maje ya kuma ce, kungiyar na mika jinjina ta musamman ga Tsohon Gwamnan Jigawa Barrister Ali Sa’adu Birninkudu, Kwamishinan Labarai, Wasanni da Matasa, Malam Bala Ibrahim Mamsa, Kwamishinan Noma, Kanal Alhassan Muhammad Mai Ritaya, Kwamishinan Kudi, Alhaji Babangida Umar Gantsa, Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Alhaji Garba Hannun Giwa, Kwamishinan Ilimi, Dr. Lawan Yunusa Danzomo da kuma Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Alh Magaji Yusuf Gigo, da ma duk wadanda suke baiwa kungiyar gudunmawa a jihar Jigawa da kasa baki daya.

Domin samun karin bayani game da Kungiyar Manoman Citta ta Kasa reshen jihar Jigawa za ku iya tuntubar Shugaban Kungiyar Ado Maje Saleh (Retd) a kan wannan lamba: 0902 927 7717

Comments
Loading...