For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

NPOWER Ta Tabbatar Da Kudirinta Na Fara Bayar Da Horo Ga Wadanda Ta Yaye

Ma’aikatar Kula da Aiyukan Jin Kai, Magance Annoba da Samar da Cigaban Al’umma karkashin Minista Sadiya Umar Faruk ta tabbatar da shirinta na fara bayar da horo na musamman ga ‘yan NPOWER na Batch A da B wadanda ta yaye domin sallamarsu.

Ma’aikatar ta nuna cewa, a watannan na Fabarairu ne za ta fara aiwatar da kashi na farko na wannan aiki.

Ana sa ran za a horar da wadanda aka yaye din a fannin sana’o’i da dabarun kasuwanci domin su dogara da kansu.

Ma’aikatar ta yi kira ga duk wadanda sukai aikin NPOWER a Batch A na shekarar 2016 da kuma ‘yan Batch B na shekarar 2017 da su tura sakon wayar salula domin shiga tsarin.

Ta umarce su da su danna wadannan lambobi a layikansu na wayar salula: *45665# su bi abin da ya biyo baya.

Sai dai kuma da dama daga cikin ‘yan NPOWER wadanda aka bukaci su dannan lambobin, sun tabbatarwa TASKAR YANCI cewa idan sun danna abin ba ya tafiya.

Comments
Loading...