Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Ifeanyi Okowa, a jiya Talata caccaki jam’iyya mai mulki, All Progressives Congress (APC), inda ya ce zabin jam’iyyar na yin tikitin Muslim-Muslim shine hukuncin rashin basira da ta yi a kasa mai banbance-banbance kamar Najeriya.
Okowa ya kuma caccaki gwamnatin Shugaba Buhari ta APC da kassara tattalin arzikin kasa tare da jefa ‘yan Najeriya cikin matsanancin talauci wanda ba sa ciki shekaru takwas da suka gabata.
Okowa ya yi wannan jawabi ne a wani taron siyasa da aka gudanar jiya a Abuja.
A wajen taron, Okowa na tare da Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, inda ya ce “Ni ban yarda da tikitin Muslim-Muslim ba. Dalili kuwa shine, akwai rarrabuwar kai idan aka ce za ai haka. Saboda haka, nacewa a kan sanya ‘yan addini guda ba abu ne mai kyau ba musamman a kasa mai cike da kalubale da muke ciki a yanzu. Abun ya yi kama da ka ce za a samu dan takarar shugaban kasa daga Arewa ne kuma ya dauko dan takarar mataimakinsa ma daga Arewa.”
Okowa, wanda shine kuma Gwamnan Jihar Delta mai ci ya ce, a dalilin wannan hukunci na APC, ba zata samu nasarar cin zaben shugaban kasa ba.
“Saboda haka, takarar da zata yiwu ga ‘yan Najeriya ita ce wadda ba ta alakanta samun nasararta ga wani addini na Musulunci ko Kiristanci ba,” in shi.
Kungiyar Matasan Kiristocin Arewacin Najeriya ce ta shirya taron mai taken, “Hada kan Najeriya: Gudunmawar Kiristoci Matasa da Mata na Arewa.”
Okowa ya fadawa matasan cewa, da goyon bayansu, jam’iyyar PDP zata samu nasara a zabukan shekarar 2023.