Gwamnan Jihar Delta, Dr. Ifeanyi Okowa, jiya Juma’a a Asaba, ya sanya hannu a kudirin kasafin kudin jihar na shekarar 2023 mai yawan naira biliyan 571, abin da ya mayar da kudirin doka.
Kasafin kudin wanda shine na karshe a matsayinsa na gwamna, ya hada da naira biliyan 235.5 na aiyukan yau da kullum da kuma naira biliyan 336.1 na manyan aiyuka.
Haka kuma Gwamna Okowa ya sanya hannu a wasu kudire-kudiren dokar guda tara da suka hada da Dokar Jihar Delta ta Masana’antu da Anfani da Jiragen Ruwa na Cotonou; Dokar Jihar Delta ta Kula da Kudaden Al’umma; Dokar Jihar Delta ta Kariya da Hana Cin Zarafin Masu Dauke da HIV/AIDS; Dokar Jihar Delta ta Harajin Hanyoyin Ruwa da Baiwa Komaye Lasisi ta 2022 da sauransu.
KARANTA: Rikici Ya Barke A Jam’iyyar APC Kan Dakatar Da Tsohon Gwamna
Da yake jawabi bayan sanya hannu a kan kudire-kudiren, Okowa ya bayar da tabbacin cewa jihar zata yi kokari wajen aiwatar da manyan aiyukan da ke kasafin shekarar mai kamawa sannan ta karasa aiyukan da ake kan yi kafin karewar wa’adinsa.
Ya yabawa Majalissar Jihar bisa hadin kan da take baiwa gwamnatinsa tsawon shekaru, inda ya ce, gwamnatin tasa ba ta samu nasara ba sai da gudunmawar majalissar da al’ummar Jihar Delta.
Ya ce, “Ku sami lokaci ku yi aiki kan wadannan kudire-kudire, duk halin yakin neman zabe da ake ciki, ya nuna cewa, kun tsaya tsayin-daka kan bukatun al’ummarmu da suka zabe ku.”
Da yake gabatar da kudire-kudiren, Kakakin Majalissar Jihar, Chief Sheriff Oborevwori ya ce, kudire-kudiren sun bi duk hanyoyin tabbatar da doka da ake bi kafin a amince da su.
Ya nuna jin dadinsa ga gwamnan da sauran mambobin majalissar bisa gudunmawa da hadinkan da suka bayar tsawon shekaru a matsayinsa na kakakin majalissar mafi tsayin lokaci.