For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Orji Kalu Ya Zama Sanata Mafi Yin Aiyukan Raya Kasa Ga ‘Yan Mazabarsa A 2022

Bulaliyar Majalissar Dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu ya zo na daya a Gasar Sanata Mafi Aiyukan Raya Kasa da Iya Jagoranci ta shekarar 2022.

A wani zabe da aka gudanar a duk fadin Najeriya ta yanar gizo wanda Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN ya bibiya, Kalu wanda ke wakiltar mazabar sanata ta Abia North, ya samu kuri’u 283,011 inda ya doke sauran sanatoci a gasar.

Cikin sauran sanatocin, Sanata Ovie Omo-Agege ya samu kuri’u 128,330, yayinda Sanata Adetokumbo Abiru ya samu kuri’u 83,204, sai Sanata Barau Jibrin wanda ya samu kuri’u 72,276.

Gasar dai gidan talabijin mafi yiwa al’umma hidima a Afirka, Igbere TV ne ya shirya da samun goyon bayan African Union da kuma African Film Institute.

Tsohon Gwamnan Jihar Abia, Orji Kalu, wanda aka zaba a sanata a shekarar 2019, ya samu nasarar jawowa mazabarsa ta Abia North aiyukan tituna kimanin 50 cikin shekaru 3.

Wasu daga cikin aiyukan da Kalu ya samawa mazabarsa sun hada da tituna masu tsawon kilomita 2 zuwa biyar a duk kananan hukumomi 5 da ke mazabarsa; gyaran makarantu da asibitoci; samarwa dalibai kayan koyon karatu; raba kekunan dinki, janaretoci da babura kimanin 1000 ga manoma da masu sana’o’i da ma sauran abubuwan ci gaba.

NAN  

Comments
Loading...