For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Osinbajo Ne Jagoran Najeriya Yanzu Bayan Buhari Ya Tafi London Neman Magani

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya baiyana cewa Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo shi ke da ikon gudanar da Najeriya a halin yanzu.

Shugaban ya baiyana hakan ne yau Lahadi lokacin da yake barin Abuja da nufin zuwa London domin a duba lafiyarsa.

Har dai zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a tantance ko cewa Buhari ya aikewa Majalissar Tarayya wasikar bayar da mulki ga mataimakin nasa ba zuwa lokacin dawowarsa kasar.

Lokacin da aka tambaye shi ko tafiyar tasa za ta shafi gudanuwar al’amura a kasar, Buhari ya ce, “Da ma ai ba ni kadai nake yin wannan aikin ba. Akwai cikakken wakilcin gwamnati. Mataimakin Shugaban Kasa yana nan.

“A tsarin kundin tsarin mulki, lokacin da ba na nan, shi ke jagoranci. Sannan muna da Sakataren Gwamnatin Tarayya ga kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa. Saboda haka babu wata matsala.”

(PUNCH)

Comments
Loading...