For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Osinbajo Ya Yi Fatan Alheri Yayinda Buhari Ke Cika Shekaru 80 A Duniya

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, SAN, tare da matarsa, Dolapo Osinbajo, sun taya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari murnar zagayowar cikar shekararsa, inda yake cika shekaru 80 a ranar Asabar din nan 17 ga watan Disamba, 2022.

A jawabin da shi da kansa ya sanyawa hannu, Osinbajo ya rubuta: “Happy 80th Birthday, Mr. President!

“Rayuwarka ta musamman, ta yiwa kasa hidima a matsayin soja, a matsayin gwamna, a matsayin minista, a matsayin shugaban mulkin soja da kuma a matsayin shugaban kasa na farar hula na wa’adi biyu ya nuna cewa, abu ne mai yiwuwa a yiwa kasa hidima da al’umma cikin riko da gaskiya, ba tare da son zuciya ba.

“Dolly da ni, da iyalaina muna yi maka fatan samun karin shekarun farinciki cikin zaman lafiya da lafiyar jiki, da sunan Jesus. Amin.”

Comments
Loading...