For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

PDP Da APC Sun Raba Kujerun Kananan Hukumomin Abuja A Zaben Da Aka Kammala

Jam’iyyar All Progressives Congress, APC, da jam’iyyar People’s Democratic Party, PDP, sun raba kananan hukumomin Abuja daidai wa daida inda kowaccensu ta ci kananan hukumomi 3 a zaben da aka gudanar jiya.

APC ta ci kananan hukumomin Gwagwalada, Kwali da kuma Abaji, yayinda ita kuma PDP ta ci kananan hukumomin Abuja Municipal Council Area (AMAC), Kuje da kuma Bwari.

A karamar hukumar Kuje, dan takarar PDP, Suleman Sabo, ya samu kuri’u 13,301 wanda hakan ta sa ya kayar da dan takarar APC, Sarki Hamidu wanda ya sami kuri’u 7,694.

A karamar hukumar Gwagwalada kuma, dan takarar APC, Jubrin Abubakar wanda tsohon shugaban karamar hukumar ne, ya kara lashe zaben.

Jubrin ya samu kuri’u 11,125 wanda hakan ta sa ya doke abokin hamaiyarsa na jam’iyyar PDP, Mohammed Kassim wanda ya samu kuri’u 9,597.

A karamar hukumar Bwari kuma, dan takarar PDP, John Gabaya ne ya lashe zaben.

Hukumar INEC ta baiyana cewa John ya samu kuri’u 13,045 abin da ya sa ya doke abokin karawarsa na jam’iyyar APC, Audi Shekwolo wanda ya sami kuri’u 7,697.

Dan takarar jam’iyyar PDP, Christopher Zakka ne ya lashe zaben a karamar hukumar Birnin Abuja.

Christopher ya samu kuri’u 19,302 abin da ya sa ya doke abokin hamaiyarsa na jam’iyyar APC, Murtala Usman, wanda ya samu kuri’u 13,240.

A karamar hukumar Kwali kuma, dan takarar APC, Danladi Chiya ne ya lashe zaben.

Ya samu kuri’u 7,646 abin da ya ba shi damar kayar da abokin hamaiyarsa na jam’iyyar PDP, Haruna Pai wanda ya sami kuri’u 7,345.

A karamar hukumar Abaji an baiyana jam’iyyar APC a matsayin wadda ta samu nasara ba tare da sunan dan takara ba.

Hukumar INEC ta baiyana cewa, jam’iyyar APC ta samu kuri’u 7,289 inda ta kayar dan takarar jam’iyyar PDP, Alhaji Yahaya Garba Gawu wanda ya sami kuri’u 4,062.

Hukumar ta ce za a baiyana sunan wanda ya ci zaben bayan an yanke hukunci kan shari’ar da ake yi mai alaka da zaben a wata kotu a Abuja.

Dan takarar shugaban karamar hukumar Abaji daga jam’iyyar APC, Abubakar Umar Abdullahi, ya daukaka kara zuwa Kotun Koli bayan Babbar Kotun Abuja da Kotun Daukaka Kara sun soke takararsa tare da baiyana Alhaji Mohammed Angulu Loko, a matsayin halastaccen dan takarar jam’iyyar APC a karamar hukumar ta Abaji.

Comments
Loading...