Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP ta nemi tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo da ya faiyyace bayaninsa na kwanannan inda ya bayyana nadamar zabar Atiku Abubakar a matsayin mataimakinsa a shekarar 1999.
Obasanjon dai a lokacin da yake jawabi a taron horas da wasu dalibai a Abeokuta da ke Jihar Ogun kan harkar mulki a ranar Asabar da ta gabata, ya ce daukar wanda zai mara masa baya a matsayin mataimaki lokacin da yake son zama shugaban kasa a 1999 na daya daga cikin abubuwan da ya yi na kuskure a rayuwarsa.
“Wani abu da ya faru da ni shine, Allah bai yasar da ni ba, wannan kuma muhimmin abu ne. Misali, daya daga cikin kuskuren da na yi shine daukar wanda zai zame na biyu lokacin da zan zama shugaban kasa,” in ji Obasanjo.
Atiku Abubakar, wanda shine yake yi wa jam’iyyar PDP takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 mai zuwa, shine ya kasance mataimakin shugaban kasa a lokacin mulkin Obasanjo wanda ya gudana tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.
Da yake jawabi ga ‘yan jarida a ranar Litinin, shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, Walid Jibrin, ya nemi tsohon shugaban kasar da ya faiyace abun da yake nufi da maganarsa cikin awanni 48.
“Hankalinmu ya kai kan maganar da aka ce Cif Olusegun Obasanjo, tsohon Shugaban Kasa ya yi, cewa kuskure ya yi da ya dauki Atiku Abubakar a matsayin mataimakin shugaban kasa a 1999,” in ji shi.
Walid Jibrin ya ce, duk da dai Obasanjo bai ambaci sunan Atiku karara ba, bayanai kan abun da ya fadawa masu sauraronsa na nuni da cewa yana nufin tsohon mataimakin shugaba kasa.
“Obasanjo ya fito ya faiyace jawabinsa – ko ba a rawaito jawabin dai-dai ba, ko kuma yana nufin abun da ya fada,” in ji Walid Jibrin.
“Lokacin da ya faiyace jawabin ne jam’iyyar PDP zata mayar masa da martani.
“Wani zai iya tunanin abun da ya fada dai-dai ne, amma kuma muna so mu ba shi lokaci zuwa gobe (Talata) ko jibi (Laraba). Idan ya fito ya ce ba a ji jawabinsa dai-dai ba ko ya ce yana nufin abun da ya fada a kan Atiku, to zaku ji tonon silili domin kuwa zan fasa kwai.
“Zan kuma fadawa ‘yan Najeriya da ma duk duniya waye Obasanjo, ta yaya Atiku ya temake shi wajen shugabancin Najeriya da kuma yanda Atiku ya hana shi yunkurin zarcewa karo na uku a mulki.
“Saboda haka, yana da matukar muhimmanci mu ji daga Obasanjo karara.”