For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

PDP Ta Dage Zaben Shugabanninta Na Arewa Maso Yamma

Jam’iyyar PDP ta dage zaben shugabanninta na yankin Arewa maso Yamma wanda da aka shirya gudanarwa ranar 12 ga watan Fabarairun da muke ciki a Kaduna.

Mamba na Kwamitin Rikon Jam’iyyar PDP a yankin Arewa maso Yamma, Muhammad Akibu Dalhatu ne ya baiyana haka a tattaunawarsa da wakilin NIGERIAN TRACKER, tattaunawar da jaridar TASKAR YANCI ta bibiya.

Muhammad Akibu ya ce, sun sami rahoton sirri na wasu mutane da suke son tayar da zaune tsaye a lokacin zaben saboda tunanin cewa dan takarar da suke so ba zai ci zaben ba.

Ya baiyana cewa, tun da jam’iyyar PDP a yankin Arewa maso Yamma tsintsiya ce madaurinki daya, to akwai bukatar a gudanar da zaben a cikin yanayi na nutsuwa ba tare da rikici ba.

Muhammad Akibu ya kuma ce, labaran da ke zagayawa cewa, akwai umarnin kotu da zai hana gudanar da zaben ya yi nesa da gaskiya.

Ya kara da cewa, akwai wadansu gun-gun mutane a yankin Arewa maso Yamma musamman daga jihar Kano wadanda suke son a yi sasanto duk da cewar an ba da damar cewa mataimakin shugaban jam’iyyar daga yankin, an buda shi ga kowa amma sun matsa kan sai an yi sasanto wato consensus.

Ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su yi hakuri tare da bayar da hadin kai har kwamitin rikon ya baiyana wata ranar.

Comments
Loading...