For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

PDP Ta Kalubalanci Buhari Da Ya Tona Asirin Masu Tallafawa Ta’addanci

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a jiya, ta ce kin amincewar gwamnatin tarayya na tona asirin masu daukar nauyin ta’addanci a Najeriya ya tabbatar da matsayin ta cewa gwamnatin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tana “ba da kariya ga ‘yan ta’adda da ‘yan fashi da ke ruguza kasar.”

Babbar jam’iyyar adawar ta ce matsayinta ya biyo bayan “sanarwar da fadar shugaban kasa Buhari ta fitar cewa ba ta da sha’awar bayyana a bainar jama’a da sunayen ‘yan Najeriya shida da rahotanni suka bayyana cewa Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta aikawa gwamnatin a matsayin masu daukar nauyin ta’addanci a kasarmu.”

PDP a cikin wata sanarwa daga sakataren yada labaranta na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar, ya ce “matakin da gwamnatin APC ta dauka na rufe sunan wadanda ke daukar nauyin kashe-kashen, fyade, garkuwa da ‘yan uwanmu, da ma rikice-rikicen tashin hankali tsakanin al’ummomin karkashin kulawar APC, yana tabbatar da matsayin mu na cewa irin wadannan mutane suna da alaka da jam’iyyar ta APC.”

PDPn ta ci gaba da cewa: “wannan matsayin na rashin nuna kishin kasa daga shugaban kasa Buhari yana sa matsananciyar damuwa tare da nuna irin hannun da gwamnatin ke da shi wajen lalata tsarin tsaron da kawo karuwar kashe-kashe da ayyukan ta’addanci a cikin shekaru shida na karkashin jam’iyyar APC.”

Jam’iyyar ta ce a koyaushe tana nuni game da “alakar da ke tsakanin APC da ‘yan ta’adda da ke lalata sassa daban -daban na kasar da yadda APC a matsayinta na jam’iyya a koda yaushe ta gaza yin tir da ayyukan ta’addancin a kasarmu.”

Da yake mai da martini, mai ba Shugaban Kasa Shawara ta Musamman kan Kafafen Yada Labarai, Femi Adesina, ya bayyana cewa gwamnati mai ci yanzu ba ta da sha’awar bayyana suna ko kunyatar da masu daukar nauyin Boko Haram da sauran masu tallafawa ayyukan ta’addanci a fadin kasar.

Mai taimakawa shugaban ya ce a maimakon haka, gwamnati ta mai da hankali wajen gabatar da “masu laifin” a gaban shari’a. Ya yi wannan maganar ne jiya da yamma a matsayin bako a shirin ‘Politics Today’.

Tun da farko an ba da rahoton cewa Hadaddiyar Daular Larabawa ta ambaci sunaye da kuma gurfanar da wasu ‘yan Najeriya shida da ma wasu 32 saboda zarginsu da tallafa wa ta’addanci.

Da aka tambaye shi bayani game da gurfanar da masu daukar nauyin ta’addanci a cikin kasar, Adesina, wanda ke cikin rakiyar Shugaba Buhari a New York don Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya, ya ce: “Bayyana suna da kunyatarwa ba za su zama mafiya muhimmanci ba, abin da zai fi shine a gabatar da su gaban kuliya.”

Comments
Loading...