For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

PDP Ta Rushe Tsarin Karba-Karba A Takarar Shugaban Kasa

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa masu sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar na iya fitowa daga kowanne bangare na Najeriya ba tare da dogaro da yankin da mutum ya fito ba.

Wannan na nuni da cewa, dadaddiyar al’adar nan da aka san jam’iyyar da ita ta karba-karba tsakanin yankin Arewa da Kudancin Najeriya ta zo karshe.

Sai dai a daya hannun kuma wani cincirindon matasa sun cika kofar ofishin Jam’iyyar suna zanga-zanga a kan lalle ya kamata PDP ta yiwa Arewacin Nigeria adalci ta fitar dan takarar shugaban kasa daga yankin  Arewa, domin a cewar su shekaru 13 yankin Kudu ya kwashe yana mulkin Najeriya a karkashin Jam’iyyar, yayin da yankin Arewa yai shekaru biyu kacal.

A wani abu mai kama da an gudu ba a tsira ba, jam’iyyar ta amince da karba-karbar a bangaren shugabancin jam’iyyar a matakin kasa.

Jam’iyyar ta amince da rahoton kwamitin duba karba-karba da gwamnan Enugu, Lawrence Ifeanyi Ugwuanyi ya jagoranta ya gabatar, na cewa shugaban jam’iyyar ya fito daga bangare Arewa.

Rahoton kwamitin dai ya nuna cewa, dukkanin kujerun da a yanzu ke bangaren Kudancin kasar za su koma bangaren Arewa, haka su ma wadanda ke bangaren Arewacin kasar za su koma bangaren Kudu a babban zaben jam’iyyar da za a gabatar ranar 30 zuwa 31 ga watan Oktoba.

Hukunce-hunkucen jam’iyyar dai sun biyo bayan tarurrukan da  manya manyan kwamatocin Jam’iyyar suka gudanar a ranar Alhamis din nan a ofishin Jam’iyyar na kasa dake Wadata Plaza, Abuja.

Akwai jita-jitar cewa tsohon shugaban Majalissar Dattawan Nigeria Sen. David Mark da wasu Tsoffin Gwamnonin Jihohin Jigawa, Sule Lamido da na Katsina Ibrahim Shehu Shema suna daga cikin na gaba-gaba wajan neman Shugabancin Jam’iyyar na kasa.

Yanzu haka dai Jam’iyyar PDP ta tabbatar da ranar 30 ga watan Oktoba na 2021 a matsayin ranar da za ta gudanar da Babban Taronta na kasa domin fitar da shugabannin da zasu jagoranci jam’iyyar zuwa babban zaben shekarar 2023.

Comments
Loading...