For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

PDP Ta Sa Miliyan 5 A Matsayin Kudin Form Na Takarar Shugabancinta

Jam’iyyar PDP ta sanar da fitar da jadawalin kudaden takardun neman takara a babban zabenta da ke kusantowa.

Kwamitin shirya taron ya sanar da fara siyar da takardun neman takarar a yau Litinin.

An sanya kudin form din mai neman tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar a kan farashin Naira Miliyan 5, yayin da na matemakin shugaban jam’iyyar da kuma sakataren jam’iyyar na kasa a kan Naira Miliyan 3 kowannensu.

Su kuma kudaden takardun neman takarar ofisoshin Sakataren Yada Labarai na Kasa, Odita na Kasa, Sakataren Kudi na Kasa, Shugaban Matasa na Kasa, Ma’aji na Kasa, da Mai Bayar da Shawara kan Harkokin Shari’a na Kasa duk za a sayar da su a kan Naira Biliyan 2 kowannensu.

Kudin takardun neman takarar mataimakan wadanda aka ambata kuma dukkanninsu za a siyar da su a kan Naira 750,000.

Shugaban Kwamitin Shirya Babban Taron jam’iyyar PDP na kasa, Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya bayyana cewa  za a gudanar da babban taron a filin taro na Eagle Square da ke Abuja, yayin da za a tantance ‘yan takarkaru a Old Parade Ground, da ke Area 10, Abuja.

Jam’iyyar PDP ta sanya 30 da 31 ga watan Octoba masu zuwa a matsayin ranakun da za ta gabatar da babban taron nata.

Comments
Loading...