Jam’iyyar PDP ta sanya ranar gudanar da zaben shugabanninta da ya rage ba tai ba a yankin Arewa maso Yamma.
PDP ta sanya ranar Asabar 12 ga watan Fabarairun wannan shekara a matsayin ranar da za ta zabi shugabannin jam’iyyar na yankin Arewa maso Yamma.
Sakataren Tsare-Tsaren PDP na Kasa, Hon. Umaru Bature ne ya saki wannan sanarwar a ranar Alhamis da ta gabata.
KU KARANTA: APC Ta Sa Ranar 25 Ga Fabarairu Domin Zaben Shugabaninta Na Kasa
Takardar da ya saki ta nuna cewa, wannan ya biyo bayan hukuncin da shugabancin jam’iyyar ya yanke a zamansa na ranar Larabar da ta gabata.
Umaru Bature, ya bayyana cewa, zaben shugabannin jam’iyyar PDP na yankin Arewa maso Yamma za a yi shi ne a ofishin shiyya na jam’iyyar da ke Kaduna.
Umaru ya kuma yi kira ga duk masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da sauran mambobi na yankin Arewa maso Yamma da su zama cikin shiri domin gudanar da zaben.