For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

PDP Ta Tura Shugabancin Jam’iyyar Zuwa Arewa

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta tura kujerar shugabancin jam’iyyar na kasa zuwa yankin Arewa.

Duk da dai jam’iyyar ba ta sanar da matsayarta kan inda kujerar shugabancin kasa, mataimakin shugaban kasa ko wasu mukaman zartarwa da na majalisa ba, akwai yiwuwar dan takarar shugabancin kasar zai fito daga yankin Kudu.

Sauran ofisoshin ba sa cikin aikin Kwamitin Duba Batun Karba-Karba na Babban Taron Jam’iyyar na Kasa.

Kwamitin ya ba da shawarar juya mukaman shugabancin jam’iyyar tsakanin Arewa da Kudu.

Zuwa karshen wannan, duk mukaman jam’iyyar na yankin Arewa yanzu za su tafi kudu; kuma wadanda ke kudu za su koma Arewa.

Shugaban kwamitin kuma gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi ne ya sanar da hakan a Abuja ranar Alhamis.

Ugwuanyi ya ce, “A karshen shawarwarin kwamitin karba -karba na PDP na kasa, an yanke hukunci kamar haka:

“Kwamitin Duba Batun Karba-Karba na Babban Taron PDP na Kasa an ba shi ikon rarraba ofisoshin matakin kasa na jam’iyyar don Takara a Babban Taron Jam’iyyar PDP da aka shirya yi a ranar 30 zuwa 31 na watan Oktoban 2021.

“Cewa aikin kwamitin bai hada da karkatar ofisoshin shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa da sauran ofisoshin zartarwa da na majalisun tarayyar Najeriya ba.

“Kuma matakin da kwamitin ya dauka na karkatar da ofisoshin shugabancin jam’iyyar ba zai taba tsarin ofisoshin zartarwa da na majalisa na jam’iyyar a Najeriya ba.

“Abu ne sannane cewa, PDP ta kasance tana raba shugabanci tsakanin Arewa da Kudancin Najeriya.

“Hukuncin kwamitin karba-karba na jam’iyyar PDP ya yi daidai da tsarin mulkin jam’iyyar kan karba -karba da jujjuya ofisoshin jam’iyyar da na kasa don samar da daidaito da adalci.”

Ya kara da cewa, “A sakamakon haka, ofisoshin da a yanzu ke shiyoyin kudancin kasar nan, wato Kudu maso Yamma, Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu, ya kamata su yi musaya da ofisoshin da yankunan Arewacin Najeriya, wato, Yankin Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.

“Muna so mu gode wa jam’iyyar, musamman Kwamitin Zartarwa na Kasa da ya kafa wannan kwamiti a ranar 9 ga Satumba, 2021 saboda zabo mu da duba cancantarmu da akai don yi wa jam’iyyarmu hidima a matsayinmu na mambobin kwamitin karba -karba.

“Za mu mika shawarwarinmu ga Kwamitin Zartarwa na Jam’iyyar ta hanyar Kwamitin Gudanarwa na Kasa.”

Comments
Loading...